Connect with us

News

Yadda Kanawa Ke Gudanar Da Sana’o’insu Duk Da Tsananin Zafin Rana

Published

on

Kano zafin Rana
Spread the love

A daidai lokacin da yanayin zafi ke kara kamari a sassan Arewacin Najeriya, birnin Kano na fuskantar matsanancin zafin rana da ya kai fiye da digiri 40 na Celsius, lamarin da ke barazana ga lafiya da jin daɗin al’umma.

Sai da, jama’ar birni da ya shahara da harkokin kasuwanci da sana’o’in hannu – na ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba, cikin juriya da sadaukarwa.

‎Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina  Tashoshin Samar Da Wutar Lantarki Masu Amfani Da Hasken Rana A Jihohin Arewa 19

Hukumar Hasashen Yanayi ta Ƙasa (NiMet) ta bayyana cewa Jihar Kano na cikin jerin jihohi 18 da za su fuskanci “tsananin rashin jin daɗi saboda zafi” a cikin wannan lokaci na zafi mai kamari.

Advertisement

Malam Abdullahi Ibrahim, direban adaidaita sahu mai shekaru 32, ya bayyana yadda zafin rana ke shafar aikinsa. “Tufafina yana jikewa da gumi kafin ƙarfe 12 na rana,” in ji shi. “Ina kashe kuɗi sosai wajan  siyan ruwa kamar sau uku kullum nake sayen pure water don gujewa bushewar jiki.”

A kasuwar Sabon Gari da manyan titunan jihar Kano, ‘yan kasuwa da fasinjoji na bayyana irin yadda zafin rana ke hana su sakat.

Wani likita daga Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya tabbatar da karuwar masu fama da cututtuka irin su bushewar jiki, sunstroke da ciwon zuciya.

Advertisement

Haka zalika KANO TIMES  ta ruwaito cewa yara  kanana, tsofaffi, da masu larurar numfashi sune  sukafi shiga  hadari a wannan lokacin.

A cewar masanin muhalli Injiniya Salisu Adamu daga Green Initiatives Africa, tsarin gine-ginen birnin Kano yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke haddasa dumamar yanayi. “Yawaitar ginin da ke rufe filayen ƙasa da rashin bishiyoyi yana hana iska zagayawa yadda ya kamata,” in ji shi.

A wani mataki na rage tasirin wannan matsala, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da shirin dasa bishiyoyi miliyan uku a fadin jihar. Masana sun ce wannan matakin na da tasiri mai kyau idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata.

Advertisement

Sai dai matsalar rashin wutar lantarki na ci gaba da dagula al’amura, inda mutane ke fuskantar ƙalubale wajen samun ruwan sanyi, amfani da fanfo ko kayan sanyaya daki, lamarin da ke ƙara jefa su cikin damuwa.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *