News
Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Tashoshin Samar Da Wutar Lantarki Masu Amfani Da Hasken Rana A Jihohin Arewa 19
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana shirin ta na gina tashoshin samar da wutar lantarki masu amfani da hasken rana a jihohi 19 na arewacin ƙasar. Wannan mataki na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunkasa makamashi mai tsafta da kuma inganta wutar lantarki a ƙasar.
Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ne ya sanar da hakan yayin taron manema labarai karo na shida na shekarar 2025 da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis. Ya bayyana cewa an tsara gina tashoshin da za su samar da jimillar megawatt 1,900 na lantarki daga hasken rana, inda kowace tasha za ta samar da megawatt 100.
Sabuwar Ƙungiyar Ta’addanci Ta Bayyana A Arewa , Sun Kashe Fiye Da Mutane 15
Ministan ya kara da cewa burin gwamnatin tarayya shi ne samar da kusan megawatt 8,000 na lantarki kafin ƙarshen zangon mulkin Shugaba Tinubu a shekarar 2027.
”Wannan tsari zai taimaka wajen bai wa jihohi damar dogaro da kai a fannin wutar lantarki, tare da rage dogaro da babban tsarin rarraba wutar ƙasa,” in ji Adelabu.
A cewarsa, gwamnati na kuma ci gaba da lalubo hanyoyin jawo hankalin masu saka hannun jari masu zaman kansu domin fadada da inganta cibiyar samar da wutar lantarki ta ƙasa.
Shirin ya zo a daidai lokacin da matsalolin yawan yanke wuta ke ci gaba da damun al’umma, musamman a arewacin ƙasar, inda barna ga layukan wutar lantarki da sata suka haddasa tsawon lokaci ba tare da wuta ba.
A watan Oktoba na shekarar da ta gabata, barayin kayayyakin lantarki sun lalata layin wuta mai karfin 330kV daga Shiroro zuwa Kaduna, wanda ke samar da wuta ga jihohin Kaduna da Kano da wasu sassa na arewa maso gabas. Wannan ya jefa akalla jihohi 17 cikin 19 na Arewa cikin duhu har na tsawon wata guda.
Biyo bayan haka, gwamnonin jihohin Arewa 19 sun bukaci samar da hanyoyin samar da wutar lantarki masu zaman kansu domin magance matsalar yawan yanke wuta da inganta rayuwar al’umma.
Jihohin da za su amfana da shirin sun hada da: Neja, Kwara, Kaduna, Kano, Jigawa, Gombe, Katsina, Sokoto, Zamfara, Bauchi, Yobe, Borno, Adamawa, Taraba, Filato, Nasarawa, Kogi, Benue da Kebbi.
Ministan ya jaddada cewa Najeriya na da isasshen hasken rana da zai iya maye gurbin hanyoyin samar da wutar lantarki masu gurbata muhalli. Ya ce wannan dama ce da ƙasa ke da ita wadda dole ne a yi amfani da ita yadda ya kamata.
PRNIGERIAN
