News
SERAP Ta Maka NBC A Kotu Kan Haramcin Wakar Eedris Abdulkareem “Tell Your Papa”
Kungiyar kare hakkin dan Adam da duba daidaito a harkar mulki, wato SERAP (Socio-Economic Rights and Accountability Project), ta shigar da kara a gaban Kotun Tarayya da ke Legas tana kalubalantar haramcin da Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye ta Kasa (NBC) ta sanya kan wakar fitaccen mawakin nan, Eedris Abdulkareem, mai taken “Tell Your Papa.”
A cewar SERAP, umarnin NBC na ranar 9 ga Afrilu, 2025, wanda ya haramta wa dukkan gidajen watsa shirye-shirye a Najeriya saka wakar, ya saba wa doka kuma take ne ga ‘yancin fadin albarkacin baki. Kungiyar ta bukaci kotu da ta soke wannan haramci tare da bayar da umarnin haramcin dindindin da zai hana NBC ko wani mutum ko hukuma hana watsa wakar a kafafen yada labarai.
Yadda Kanawa Ke Gudanar Da Sana’o’insu Duk Da Tsananin Zafin Rana
SERAP ta bayyana cewa haramcin da NBC ta sanya yana karya hakkokin dimokuradiyya na fadin albarkacin baki, samun bayanai da ‘yancin yada labarai. A cikin rantsuwar shaida da aka gabatar a gaban kotu, kungiyar ta ce dalilin kare tarbiyya da dabi’a da NBC ke amfani da shi wani hani ne da ba shi da tushe a tsarin mulki.
Kungiyar ta jaddada cewa wakar “Tell Your Papa” tana dauke da muhimman sakonni da suka shafi yadda ake tafiyar da mulki a kasar, kuma ko da bayanan cikin wakar na iya bata rai ko tayar da hankali, hakan ba hujja ba ce da za ta hana fadin ra’ayi a karkashin dimokuradiyya.
SERAP ta ce Sashen 3.1.8 na dokar NBC ya wuce gona da iri, yana keta hakkokin ‘yan kasa, kuma haramcin wakar Eedris ba ya bin ka’idojin da suka kamata. A cewarta, sharadin kare tarbiyya ya zama makarkashiyar dakile wakar da kuma take ‘yancin ‘yan Najeriya wajen bayyana ra’ayoyinsu cikin ‘yanci da walwala.
Kotun dai har yanzu ba ta nada alkalin da zai saurari karar ba, yayin da ake sa ran wannan lamari zai kara jaddada mahimmancin kare ‘yancin fadin albarkacin baki a tsarin mulki
n Najeriya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
