News
Prof. Gwarzo Ya Bai Wa NWDC Ginin Bene Mai Hawa Bakwai Domin Zama Hedikwata A Kano

A wani muhimmin mataki na tallafawa ci gaban yankin Arewa Maso Yamma, shugaban kuma wanda ya kafa Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya mika wani gini mai hawa bakwai ga Hukumar Ci Gaban Arewa Maso Yamma (NWDC), domin amfani da shi a matsayin hedikwatar hukumar na wucin gadi a Kano.
Wannan gagarumar kyauta an mika ta ne a hukumance ta hannun Shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, wanda ya wakilci Farfesa Gwarzo a yayin wani gajeren bikin da aka gudanar a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, 2025.
An gudanar da bikin ne a harabar ginin dake lamba 16c a titin Murtala Mohammed, Kano.
SERAP Ta Maka NBC A Kotu Kan Haramcin Wakar Eedris Abdulkareem “Tell Your Papa”
Da yake bayyana manufar wannan kyauta, Farfesa Gwarzo ya ce gudummawar ta kasance wani ɓangare ne na kokarinsa na tallafawa hukumar NWDC domin ta fara gudanar da aikinta cikin hanzari da inganci, musamman duba da mahimmancin aikinta ga cigaban yankin Arewa Maso Yamma.
A nasa jawabin, Shugaban kuma Babban Darakta na NWDC, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ya bayyana jin dadinsa da godiya ta musamman ga Farfesa Gwarzo da shugabancin MAAUN bisa wannan gagarumar gudummawa. Ya ce ginin zai bayar da dama ga hukumar da aka kafa kwanan nan ta fara aiki ba tare da jinkiri ba.
“Ina son yin amfani da wannan dama domin nuna godiya ga wanda ya kafa MAAUN bisa wannan kyauta mai muhimmanci da za ta bai wa hukumar damar fara aiki nan take,” in ji Farfesa Ma’aji.
Taron mika ginin ya samu halartar wasu muhimman baki ciki har da Shugaban Gudanarwa na African International School of Development (AISD), Audu Muhammad Liman, da manyan jami’an NWDC da MAAUN da sauran baƙi masu daraja.
