Business
Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka NCC ta maka Kamfanin MTN A kotu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar Kare Haƙƙin Mallaka ta Nijeriya, NCC, ta gurfanar da Kamfanin Sadarwar MTN da wasu mutane huɗu a gaban kotu bisa zarginsu da keta haƙƙin mallaka.
An shigar da aarar mai lamba FHC/ABJ/CR/111/2024 a babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Litinin.
MANHAJA ta ruwaito cewa Sauran mutane huɗu da ake tuhuma a shari’ar su ne; Karl Toriola, shugaban MTN na Nijeriya, Nkeakam Abhulimen da Yahaya Maibe.
A cikin tuhume-tuhume uku, NCC ta yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar, a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2017, “sun amfani da fasahar da ba tasu ba”, sun keta ayyukan waƙa na wani mawaƙi, Maleke Idowu Moye ba tare da izininsa ba.
Hukumar ta yi zargin cewa waɗanda ake tuhumar sun yi amfani da ayyukan kaɗe-kaɗe da faifan sauti na Maleke a matsayin ‘Caller Ring Back Tunes’ ba tare da izinin mai fasahar ba.
Haka zalika jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ayyukan qida da faifan sauti na mawaƙin da ake zargin an keta su sun haɗa da; 911, Minimini-wanawana, Stop racism, Ewole, 911 instrumental, Radio, Low waist, kuma Babu damuwa.
An kuma zargi waɗanda ake tuhumar da raba ayyukan waƙoƙin ga abokan hulɗarsu, ba tare da izini ba, wanda hakan ya saɓa wa haƙƙoƙin mawaƙin.
A cewar NCC, laifuffukan da ake zargin sun saɓa wa sashe na 20 (2) (a) (b) da (c) na dokar hakkin mallaka, Cap. C28, Dokokin Tarayyar Nijeriya, 2004.
Har yanzu dai ba a sanya karar ga kowane alƙali ba kuma ba a ƙayyade ranar da za a fara shari’ar ba.