News
Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 279 Tare Da Ƙwato Haramtattun Ƙwayoyi A Kaduna
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun yi nasarar kama mutane 279 da ake zargi tare kuma kwato haramtattun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 2,092.5 a rubu’in farko na shekarar 2024.
Kwamandan hukumar ta NDLEA reshen jihar Kaduna, Mista Samaila Danmalam shi ne ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a ranar Asabar .
El-Rufai Ya Jibge Min Bashin $587 Da Biliyan 85 A Kaduna – Uba Sani
“A wani samamen da aka kai, hukumar ta yi nasarar kama mutane 279 da ake zargi, masu safarar miyagun kwayoyi ne,da diloli da kuma masu amfani da su yayin da jami’ai suka tarwatsa gidajen saida haramtattun kwayoyi 39 a wurare daban-daban na jihar.
Yace ƙwayoyin da aka kama sun haɗa da hodar iblis, heroin, wiwi, Tramadol, Methamphetamine da sauran kayan maye masu nauyin kilo 2,092.5.
Ya kuma bayyana cewa, rundunar ta samu nasarar kama mutane 48, tare da gurfanar da mutane 68 , sannan ta gurfanar da wasu 34 a cikin rubu’in farko na shekarar.
Wikki Time
-
News6 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
