News
An Cafke Wasu Mutane 3 Kan Satar Raguna 132 A Mashegu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An cafke wasu mutane uku kan laifin satar raguna 132 a karamar hukumar Mashegu da ke Jihar Neja.
Leadership ta ruwaito cewa wadanda ake zargin dai sun hada da Mohammed Abdullahi Chumo mai shekaru 30, Aliyu Salihu mai shekaru 20 da kuma Arzika Ahmadu mai shekaru 25.
RIKICIN EL-RUFAI DA UBA: APC ta dakatar da shugaban mata na jam’iyyar saboda ta goyi bayan El-Rufai
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce wadanda ake zargin sun amsa laifin ne lokacin da aka yi musu tambayoyi.
Ya bayyana cewa sun hada baki tare da sace raguna 132 a unguwar Manigi da ke karamar hukumar Mashegu.
“Abin farin ciki, a ranar 14 ga watan Maris, 2024, mai ragunan da aka yi satar, ya hangi wani da raguna guda shida daga cikin wadanda aka sace yana kokarin sayar da su,” in ji Abiodun.
Ya bayyana cewa, nan take aka kama wanda ake zargin sannan ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa kauyen Jimi inda suka boye sauran ragunan.
Daga baya rundunar ta cafke Aliyu da Arzika.
An mika su zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin gudanar da bincike.
Kakakin ‘yansandan ya kara da cewa, an mayarwa da mai ragunan dabobbinsa.