Connect with us

News

Gwamnan Zamfara ya musanta ciyo bashin naira biliyan 14.26 da DMO ta wallafa

Published

on

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya musanta cewa gwamnatinsa ta karbo bashin kudi naira biliyan 14.26.

Advertisement

Gwamnan ya kara da cewa kudaden da ake magana a kai na daga cikin rancen naira biliyan 20 da gwamnatin da ta shude ta ciwo tun a baya.

A shirye bankunan Najeriya suke wajen cika sharuɗɗan ƙarfafa jarin su -ACAMB

Premium Times ta ruwaito cewa a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya fitar, ta bayyana cewa babu rancen kuɗi da gwamnatin jihar ta karbo a cikin gida ko daga kasashen waje.

“Muna son yin karin haske kan rahoton ofishin kula da basussuka (DMO) da ta wallafa cewa gwamnatin jihar Zamfara ta ciyo bashin Naira biliyan 14.26.

Advertisement

“Gwamnatin mu ba tun rantsar da ita ba ta taba amsar bashi daga ko ina ba ko tuntubar majalisar jiha ko ta kasa domin bata dama ta ciyo ta bashi a gida ko a waje ba.

” Ina so a sani cewa gwamnatin da ta shuɗe ce ta amshi waɗannan kuɗaɗe kuma ciki ta karbi naira biliyan 4 wato cikin naira biliyan 20.

” Naira biliyan 14 da suka rage cikin kuɗin da gwamnatin da muka gada ta ciyo. Kuma kuɗin na nan ajiye ba a taɓa su ba. Za a yi amfani da su wajen gina filin jirgin saman kamar yadda aka yi niyya.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *