Connect with us

News

 Karamar Sallah : Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild na taya al’ummar Musulmi murna 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo Ta The Association of Online Media Guild na taya al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Sallah.

A cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na riko Abdullateef Abubakar Jos da sakataren kungiyar Abbas Yushau Yusuf suka fitar, kungiyar ta jaddada muhimmancin kammala kwanaki 30 na watan Ramadan cikin lumana duk da tashin farashin kayayyakin abinci da tsadar rayuwa a fadin kasar.

DA DUMI-DUMI: Jaridar Inda Ranka ta taya musulmi murnar Bakin zagayowar Karamar Sallah

Daga nan sai kungiyar ta bukaci al’ummar Musulmi a fadin Najeriya da sauran masu rutawa da tsaki da su sanya ido sosai a kan unguwanninsu a lokacin bukukuwan sallah domin kaucewa rahotannin bacewar kananan yara.

Bugu da kari, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara zage damtse wajen gyara tattalin arziki domin rage wahalhalun da talakawa ke fuskanta. Haka zalika, ta bukaci ‘yan kasuwa da su ji tsoran  tsoron Allah Ta’ala a cikin harkokinsu.

Kungiyar ta mika sakon taya murna ga shugaban kasa Bola Tinubu da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, da dukkan shugabannin gargajiya a fadin Najeriya.

Advertisement

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending