News
DA DUMI-DUMI: Jaridar Inda Ranka ta taya musulmi murnar Bakin zagayowar Karamar Sallah
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Bayan kammala ibadar azumin watan ramadan da Al,ummar musulmi sakayi na shekarar ,1445 bayan hijra annabi Muhammad (S,A,W) daga Makkah zuwa nadina jaridar inda ranka ta taya Al,ummar musulmi duniya murnar zagayowar bikin garamar sallah
Ta cikin wata takarda da Shugaban jaridar Malam KABIRU BASIRU FULATAN ya sanyawa hannu a ranar laraba kuma aka karanta a cikin afoshin,sa domin taya Al,ummar musulmi barka da sallah
A cikin takardar fulatan yace daman jaridar inda ranka jaridace daya tilo datake da San cigaban addinin musulunci tare da kawowa masu bibiyarta hirarrraki da manyan malaman duniya na domin samun rabauta ranar gobe kiyama
Haka zalika ta ƙara kira na musamman ga al’ummar ƙasar da a haɗa kai wajeyin aiki tuƙuru domin ganin cewa ansami yardar Allah da Kuma karowar zaman lafiya da yalwar arziki
“Najeriya ƙasa ce da za mu iya gina ta tayadda duk muke fata” indai munyi ayyukan alkhairi. Inji jaridar Inda Ranka.
Jaridar ta kuma yi fatan al’umma za su rungumi abubuwan nagari da suka koya a cikin watan Ramadan sa,annan su cigaba da ayyukan alkhairi ko bayan ficewar watan ramada domin cigaba da ɗabbaƙa su a kowane lokaci
Daga karshedai Shugaban ya yabawa dukkan ma,aikatan wannan jarida tare da yimusu Addu,a allah yayi riko da hannayensu allahumma Amin Tare da fatan za a yi shagulgulan Sallah lafiya.
