News
Iran Ta Harba Jirage Marasa Matuka Guda 50 Zuwa Isra’ila A Karon Farko.
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Wasu rahotanni na cewa masu kutse daga Iran sun katse wutar lantarki na birnin Telaviv na Isra’ila.
Kasar Iran ta harba jiragen yaki mara matuki a kasar Isra’ila, in ji rundunar tsaron Isra’ila, da alama wani harin ramuwar gayya da ake kyautata zaton ta kai mata.
Iran Ta Harba Jirage Marasa Matuka Guda 50 Zuwa Isra’ila A Karon Farko.
A cewar BBC gidan talabijin na Channel 12 na Isra’ila ya kuma ce ana sa ran harin zai isa Isra’ila da karfe 23:00 agogon GMT na ranar Asabar da karfe 02:00 na ranar Lahadi.
Gidan talabijin din, ya ce sojojin Isra’ila na cikin shirin ko-ta-kwana kuma suna “lura duk wani hari”.
Iran ta sha alwashin mayar da martani kan harin da aka kai ofishin jakadancinta da ke Syria a ranar 1 ga Afrilu, 2024, wanda ya kashe jami’an soji bakwai ciki har da wani babban kwamanda.
