News
Isra’ila Ta Rufe Dukkanin Makarantun Kasar Yayin Da Iran Ta Ayyana Yiwuwar Kai Na Ta Harin Na Ramuwar Gayya.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Isra’ila ta bayyana cewa ta rufe dukkanin makarantun dake kasar, a yayin da Iran ta ayyana yiwuwar kai na ta harin na ramukon gayya.
Kasar Isra’ila na rufe makarantu a fadin kasar saboda tabarbarewar tsaro, kamar yadda kakakin rundunar sojin kasar Daniel Hagari ya bayyana a ranar Asabar din nan, bayan Iran ta yi barazanar mayar da martani kan wani mummunan harin da aka kai ofishin jakadancinta na Damascus.
UTME 2024: JAMB ta gargadi masu yin jarrabawa da su kula da shafukan boge
Kasar ta ce ta dakatar da harkokin karatu a daidai wannan lokaci da ta ke cikin shirin ko ta kwata bisa la’akari da yanayin tsaro, wata sanarwa da kakakin ya fitar ta kafar talabijin ta kasar.
Iran dai ta lashi takobin mayar da martani bayan harin da ake kyautata zaton Isra’ila ta kai a ranar 1 ga watan Afrilu wanda aka yi a ofishin jakadancinta a Damascus, inda ya kashe jami’an kare juyin juya hali bakwai ciki har da janar-janar guda biyu.
