Connect with us

News

Wasu Fusattun Matasa Sun Hana Sallar Juma’a Bisa Zargin Rashin Cancantar Liman A Kano 

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

Daurawan matasa a garin jama’ar Kwagwar dake Karamar Hukumar Gezawa a jihar Kano su ka rufe babban Masallacin garin tare da hana Sabon Limamin Garin Jan Sallar Juma’a saboda zargin rashin cancantarsa .

Advertisement

A makon da ya gabata ne Alumar garin na Jama’ar Kwagwar suka zargi Dagacinsu da Hakimin Gezawa da Masarautar Gaya da Kuma Baturen Yan Sanda na Gezawa DPO da kakabawa Al’ummar garin sabon limamin da basa so saboda zargin rashin cancantarsa wato Malam Ibrahim Audu.

Yau Shekaru 17 Da Kisan Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

Dattawa da matasan garin sun yi zargin amfani da kudi wajen naɗin sabon limamamin daga Dagacin Garin zuwa fadar Hakimin Gezawa har zuwa fadar Masarautar Gaya .

Advertisement

Wikki Time ta ruwaito cewa Bayan mutuwar tsohon Limamamin Malam Aminu Ma’aruf sai Hakimin Gezawa ya nada Dansa Malam Tajudden Aminu Amma daga baya Hakimin ya warware nadin nasa aka nada wani daban saboda zargin bada cin hanci .

Tuni dai matasan garin na Jama’ar Kwagwar suka sake shirya zanga zanga tare da rufe duk wata hanya ta shiga Masallacin wanda haka yasa ba a yi sallar Juma’a a Masallacin ba a karon farko.

Advertisement

Haka kowa ya hakura ya koma gida ciki har da sabon limamamin wasu kuma sukaje masallaci mafi kusa dasu.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending