News
Jami’ar UNN ta dakatar da farfesan da aka kama yana neman lalata da dalibarsa, matar aure.
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Malamin Jami’ar, Farfesa Mfonobong Udoudom na Jami’ar Nigeria (UNN) da ke Nsukka a jihar Enugu, ya fada koman hukumar makarantar ce bayan da ya nemi yin lalata da wata dalibarsa wadda kuma matar aure ce.
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Lakcaran ya dage cewa matukar dalibarsa tasa tana son cin jarabawarsa to wajibi ne ta amince ya yi lalata da ita, in kuwa ba haka ba, to sai ya kayar da ita.
Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Tube Wasu Sarakuna Da Ta Zarga Da Taimaka Wa Ayyukan Ta’addanci
Bayanai sun ce, matar, ta sanar da mijinta halin da ake ciki, haka zalika ta kuma sanar da babban jamiin Jami’ar mai kula da harkokin dalibai (Dean Students Affairs), da kuma jami’an tsaron Jami’ar, wadanda sune suka tsara ma ta yadda lamarin zai faru domin a kama shi dumu-,dumu. Hakan kuwa aka yi, daganan sai ta wuce wajensa ta ce, ta amince da bukatarsa, inda ya sa ma ta lokacin da za ta ziyarce-shi da maraice domin ya kwashi kaya.
Bayan zuwanta sai da ya tube kayansa tumbur, sai mijin matar da jamian tsaro da Dean Students Affairs su ka shigo su ka yi ram da shi.
.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
