Connect with us

News

Siyasa Ta Shiga Hukumar Karbar Korafe-Korafe Da Yaki Da Rashawa Ta Jihar Kano – Shekarau

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya soki gwamnatocin da suka biyo bayansa akan siyasantar da ukan wasu ma’aikatun gwamnati masu mahinmanci.

Advertisement

Ya bayanawa Arewa Radiyo hakan yayin wata tattaunawa kai tsaye.

A cewarsa daya daga cikin ma’aikatun su ne hukumar karbar korafe-korafe ta jahar Kano wadda aka karkatar da akalar makasudin kafuwarta zuwa musgunawa ta siyasa a jahar.

Advertisement

Bamu Gamsu Da Sharrudan Bada Lamunin Karatu Ga ‘Yan Najeriya Ba —Malam Ibrahim Shekarau

Shekarau wanda ya kafa hukumar a zamanin mulkinsa ya bayana cewar dalilin kafa hukumar ya samu nakasu daga wasu ‘yan siyasa.

 

Advertisement

“Abun da muka maida hankali shine a tarbiyantar da mutane su daina zalinci, ina murna hukumar ta yi karfi harma hana samun manyan ‘kyasa-‘kyasai da ake kaiwa duk da dai gaskiya an bari siyasa ta shiga ciki domin duk dambarwar da akeyi kullum shugabanni ana rigima da su kan ko Gwamna ko Sarki bai kamata ba duk wannan bai taso ba, mun kafa wannan hukuma ne domin a samar da masalaha a tsakanin mutane” Inji Shekarau.

Hakazalika ya bayana damuwa akan yadda nadin mukamai da kuma aiyukan hukumar Hisbah shi ma aka siyasantar da shi domin biyan bukatar wasu ‘yan siyasan jahar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending