News
Shugaba Tinubu Ya Bawa Ministan Kuɗi Awanni 48 Ya Gabatar Da Sabon Tsarin Ƙarin Albashi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umurci Ministan Kuɗi, Wale Edun, da ya fito da jaddawalin abunda za a buƙata game da sabon mafi ƙarancin albashi cikin kwana biyu.
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa, Mohammed Idris, Shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan gwamnati bayan zaman ganawa da tawagar ta yi da shugaban kasa Tinubu a Fadar sa yau Talata.
“Cikin Mako guda an ba wa Dukkanin ɓangarorin da aka yi zaman tattaunawa da su kan sabon mafi ƙarancin albashi za su haɗu da kungiyoyin ƙwadago domin ganin an gabatar da sabon albashi ga ƴan Najeriya
“Za mu haɗu mu yi aiki ba ɓata lokaci na tsawon mako guda don tabbatar da cewa mun sami sabon albashi ga ƴan Najeriya wanda zai dawwama kuma mai inganci.”
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
