Connect with us

News

Tur Ka Tur Ka: Wata Mata Ta Kashe Ragon Laiya Da Muciya Saboda Yacinye Ƙullun Ƙosai. 

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA 

An tabbatar da mutuwar wani rago jim Kadan bayan kaisa asibiti ranga-ranga raii ga hannun Allah sakamakon shirga masa muciya har sau biyar ƙwa-ra-ra da uwargida tayi masa.

Advertisement

Wani ganau ya  shaida Jaridar Nigeria Jounals cewa saboda yacinye mata ƙullun ƙosai da take sayarwa gaba ɗaya bayan ta shiga ban ɗaki.

Bugu da ƙari mijinta ya ƙalubalanceta na aladolene ta biyashi ragon laiyarshi daya shafe tsawon lokuta yana kiwo da nufin a bana shima zaiyi laiya saboda bai taɓa yi ba.

Advertisement

Anan take dai haniya yaso ya kaure, sai dai daga gefe an samu kwamitin sulhu domin gudanar da zama na gaggawa na ganin uwargidan ta biya mijinta ragonshi data aika lahira a dalilinta na cewa yacinye mata ɗan jarin da take tattalawa wato ƙullunta na ƙosai.

Lamarin ya farune da safiyar jiya juma’a (7/6/2024) a sabuwar Anguwa ta (Kogoro Zone2 Kofar Gayan Zariya Jihar Kaduna.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending