News
Ya Kamata Gwamnatin Jahar Kano Ta Kafa Kwamiti Domin Bibiyar Malaman Makarantu Akan Dokar Da Ta Sanya

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban ƙungiyar kare hakƙin dan adam ta Universal declaration of human rights kwamared Alhaji Umar Sani Galadanchi yace ya kamata gwamnatin Jahar Kano ta kafa kwamiti domin bibiyar Malaman makarantu akan dokar da ta sanya musu na kin kar6ar kudin jarrabawa a wajen dalibai.
Kwamared Sani Ya kuma ya bawa gwamnatin Jahar Kano kan kokarin da take wajen ganin ta inganta 6angaren ilimi musamman ma ga dalibai.
Galadanchi ya kuma shawarci Malaman makarantun da suyi kokari wajen ganin sun bi dokar da aka sanya musu domin cigaban su da na Jahar Kano.
Ya kuma yi kira ga kwamishina Doguwa da ya sanar da gwamnati cewa sun samu korafi daga wasu Makarantu cewa Malaman na cewa dalibai da sukawo wasu kudade da kuma hotuna Dan yi musu rijistar jarrabawa.