Connect with us

News

Wani Lauya A Kano Ya Buƙaci Sheikh Daurawa Da Ya Daina Fitar Da Sirrin Gwamnati

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Wani Lauya mai zaman kan sa a jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ya buƙaci Shugaban hukumar Hisba na jihar Sheikh Aminu Daurawa da ya daina fadar ayyukan hukumar a gurin da bai kamata.

Lauyan mai suna Sunusi Umar Sadiq, ya yi kiran a yau juma’a a shafinsa na Facebook kamar yadda Jaridar Inda Ranka ta gani.

Advertisement

Hada-hadar kasuwanci ta ragu da kashi 33 cikin 100 a Abuja – Rahoto

Barista Sunusi Umar ya ce “Na kusa da Sheikh Daurawa ya kamata su fada ma sa duk wani abu da ya yi ko ya sani a matsayinsa na kwamandan Hisba official secret ne ba daidai ba ne ya rika fada a wurin karatu ba ko kuma ko wane yanayi da doka ba ta ba da izinin yi ba.”

Haka kuma Barista Sunusi ɗin ya ƙara da cewa “In ya na so Jama’a su san me Hisba ke ciki annual report za su rika samarwa da Jama’a.”

Advertisement

“In ka na so a yi daidai, dole ne kai ma ka yi daidai.” In ji Sunusi Umar Sadiq

WikkiTimes ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Sheikh Daurawa a lokacin haɗa wannan rahoton sai dai bai amsa kiran wayar mu ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending