Connect with us

News

Hada-hadar kasuwanci ta ragu da kashi 33 cikin 100 a Abuja – Rahoto

Published

on

 

Yawan hare-hare da farmakin ‘yan bindiga da ake fama da shi a yankunan babban birnin tarayya, Abuja da kewaye, ya haddasa taɓarɓarewar harkokin kasuwanci ya yankin.

Advertisement

Wani rahoto ya nuna cewa a Abuja kuɗaɗen shiga ko a ce ciniki ko hada-hadar kasuwanci, ya ragu da kashi 33 bisa 100.

Dattawan Arewa da na Ibo sun tsoma bakinsu kan tafiye-tafiyen Shugaba Tinubu

Kamfanin Bincike na SBM Intelligence, ya bayyana cewa matsalar tsaro da ta addabi yankin Abuja da kewaye ta haddasa tawaya ga tattalin arzikin yankin, har ya tafi da kashi 33 bisa 100.

Advertisement

Wani rahoton da SB Morgan ya fitar ya ce an samu ambaliyar ƙananan ɓarayi cikin Abuja, haka masu yi wa fasinja fashi a cikin motar haya, wato ɓarayin da ake kira ‘One Chance’, masu tsallaka gidaje su na sata sai kuma masu garkuwa da mutane, lamarin da ke nuna cewa akwai gagarimar matsala kenan ta tsaro.

Cibiyar binciken ta ce ta samu bayanan ta ne domin a hanyar jin ta bakin mazauna yankunan Abuja daban-daban. Ta ce an ji ra’yoyin su dangane da halin da ake ciki musamman ta yadda matsalar ta shafi tattalin arziki.

Advertisement

Baya ga jin ta bakin jama’a daga yankunan Abuja daban-daban, cibiyar ta ƙara da cewa ta yi amfani da rahotannin da kafafen yaɗa labarai suke bugawa, dangane da yawanitar garkuwa da mutane a Abuja da kewaye.

Sannan rahoton ya ce an samu ƙarin kuɗin haya daga kashi 10 zuwa kashi 50 bisa 100 a yankunan da ke da zaman lafiya.

Advertisement

Haka kuma rahoton ya ce matsalar garkuwa da mutane ta rage darajar gidaje da filaye da fulotai musamman a yankin Bwari da kewaye.

Masu gidajen haya na ta fama da matsalar yadda ‘yan haya ke tashi daga yankunan da ke fama da masu garkuwa da mutane.

Advertisement

Haka kuma akwai matsalar tsadar kuɗin shiga motocin sufuri, wanda ya ƙaru daga kashi 100 bida 100 har zuwa kashi 250.

Rahoton ya ci gaba da cewa tsakanin 15 ga Janairu, 2023 zuwa 15 ga Janairu 2024, an yi garkuwa da mutum 283 a yankunan Abuja da kewaye.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending