Connect with us

Politics

Masu Neman-mu Da Rikici Kuma A Gayamusu Mun Shirya  — Kwankwaso

Published

on

Dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam'iyyar NNPP sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar NNPP sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya soki gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed TINUBU wanda ya ce tana kokarin kirkiro da wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda kamar Boko-Haram a Arewa ta hanyar neman tada tarzoma a Kano.

Tsohon Gwamnan jihar ta Kano, ya ce, girke jami’an tsaro a Kano da gwamnatin tarayya ta yi sakamakon warware rawanin Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da gwamnatin Kano tayi wani yunkuri ne da ba zai haifar da ‘Da’ mai Ido ba.

Advertisement

Karancin Ruwa Na Ci Gaba Da Wanzuwa, Yayin Da Matsalar Ke Gurgunta Harkokin Zamantakewar Kanawa

“Muna da magoya baya da yawa, saboda jama’a sun yarda damu, sun yarda da akidarmu, suna da yakinin za mu yi musu asalci”

 

“Saboda haka a matsayin-mu na ‘yan siyasa ba za mu rike hannunmu mu zira ido makiyan jihar Kano su dai-dai-ta mana jiha ba, ta hanyar tayar da husuma, adon haka za mu yi duk Iya kokarin-mu don tallafawa mai girma gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ga nasara a gwamnatinsa. Ina alfahari da shi domin bai bari kokarin dagula masa lamura da makiyan jihar Kano keyi ya hana shi gudanar da ayyukan raya kasa ba” a cewar tsohon sanatan Kano ta tsakiya.

Advertisement

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wannan jawabi ne yayin kaddamar da fara aikin gina titi a yankunan karkara mai nisan kilomita 85 a yankin karamar hukumar-sa ta Madobi.

“Muna sane da wasu tsagerun mutane ‘yan jihar Kano kuma makiyan jihar wadanda munyi imani tababbu ne da suke ta shige da fice, tare da bai wa gwamnatin tarayya gurguwar shawara kan yadda za ta kwace jihar Kano da karfin tsiya ta hanyar kafa dokar tabaci, wannan dabbanci ne mafi muni wanda nayi imani mutanen jihar Kano za su bijirewa hakan” a cewar Kwankwaso.

 

Advertisement

Yayin da kakar zabe ta shekarar 2027 ke kara karatowa, akwai wasu shedanun ‘yan siyasa, makiya jihar Kano da suke ta kulle-kullen kitimurmura kala-kala da nufin dagula al’amura a jihar Kano, saboda haka mu-mun gwammace mu biyu muyi rashin nasara a bakin daga maimakon mu kyalesu su murkushemu haka kawai. Saboda haka muna kalubalantar duk wani da yake ganin zai murkushemu a siyasa da ya kwana da sanin cewa mu a shirye muke” Inji Kwankwaso.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *