News
Karancin Ruwa Na Ci Gaba Da Wanzuwa, Yayin Da Matsalar Ke Gurgunta Harkokin Zamantakewar Kanawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Matsalar karancin ruwan sha da aka dade ana fama da ita, wanda bisa ga dukkan alamu matsala ce da ta addabi kanawa haka na cigaba da gurgunta harkokin zamantakewar Al, umma.
Binciken da Jaridar PUNCH ta gudanar ya nuna cewa, biyo bayan kara tabarbarewar karancin ruwa a jihar Kano, masu sayar da ruwa sun ci gaba da cin gajiyar wannan lamari ta hanyar yin tsadar Farashin jardar ruwa, a daidai lokacin da jarka mai lita 25 ke tashi tsakanin N150 zuwa N200 mai makun a baya ta akan siyar aka naira N50 ko kuma N70.
Ƙungiyar Ɗalibai Ta Ƙasa NANS Ta Yi Alla-Wadai Da Ra’ayin Shawartar Jihohi Kan Mafi Ƙarancin Albashi
Rahotanni na nuni da cewa Unguwannin da suka fi fama da wananan matsala sun hada da yankin Kurna, Bachirawa, Fagge, Yakasai, Birged, Hotoro, da kuma Unguwar uku da ma wasu sassan kwaryar birnin Kano.
Wadanda galibinsu mazauna yankin sun dogara ne kan samar da ruwan sha na jihar, da rijiyoyin burtsatse da gwamnati ta tona da wasu masu hannu da shuni.
Wasu daga cikin mazauna yankin da suka yi magana kan halin da suke ciki, Sun bayyana rashin ruwa a matsayin abin takaici, duba da irin makudan kudaden da jihar ke kashewa wajen samar da ruwan sha a jihar.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Malam Jafar Ibrahim ya ce yana kashe kimanin Naira 2000 a kullum don siyan ruwan da iyalansa za su yi amfani da shi a gida.
Shima wani mazaunin garin Kano Abdullahi Lawan wanda abin ya shafa ya koka da matsalar karancin ruwan, wanda ya ce hakan na jefa shi cikin mawuyacin hali, saboda yanayin tafiya mai nisa domin neman ruwan da zai yi amfani da shi a gida.
Ya ci gaba da cewa, “Na kan fita ne a kowace safiya don neman rijiyoyin burtsatse ba daidaikun mutane da suka samar saboda bazan iya sayan ruwa a kan tsadar farashin da suke sayarwa ba.
Kwanan nan kwamishinan ruwa na jihar Ali Makoda ya bayyana cewa gwamnatin jihar na aiki ba dare ba rana domin ganin an samar da ruwan sha a kananan hukumomi takwas na jihar.
“Muna aiki tukuru domin ganin mun gyara matsalar karancin ruwan sha a babban birnin jihar da kewaye, kuma nan da kwanaki biyu za a kawo karshen matsalar,” inji shi.
Kwamishinan ya dora laifin kalubalen musamman kan tsofaffin kayan aiki, musamman ma a cibiyar kula da ruwa ta Tamburawa da ke samar da ruwa a cikin babban birnin Kano da kewaye.
