News
Ƙungiyar Ɗalibai Ta Ƙasa NANS Ta Yi Alla-Wadai Da Ra’ayin Shawartar Jihohi Kan Mafi Ƙarancin Albashi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa, wato NANS ta yi Alla-wadai da kiran da tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi kan tattaunawa da jihohi game da batun mafi ƙarancin albashi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kayode ya yi wannan kira ne a makon da ya gabata inda yake cewa yana ganin dacewar kowace Jiha ta tattauna da wakilan ƙungiyoyin ƙwado kan abun da zata iya biya na mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatanta.
A wata sanarwa da akawon ƙungiyar, Abdul-Yakinn Odunayo ya fitar a ranar Litinin, ya ce wannan wani mataki ne na ƙin ma’aikatan da alheri ga tsohon gwamnan.
Mafi ƙarancin albashi abu ne da gwamnatin tarayya da hukumomin ƙwadago ke tattaunawa tsawon watanni inda gwamnatin ta ce zata ke biyan 62,000 yayin da ƙungiyar ƙwadago ta kafe a kan naira 250,000.
Fayemi ya yi furucin ne la’akari da banbance-banbancen kuɗin shiga da kuma arziƙin kowace Jiha inda NANS ta ƙi amincewa da hakan tare da kira ga gwamnati da ta yi watsi da shawararsa gami da tabbatar da buƙatar ƙungiyar ƙwadago domin jindaɗi da walwalan ma’aikata.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
