Connect with us

News

Eid-el-Kabir: Ya Kamata Mutane Su Guji Cin Naman Da Ya Wuce Kima Da Zafi Domin Yana Iya Cutar Da Lafiya —Dr Labaran 

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Yayin da ake gudanar da bukukuwan Salla Babba a ko’ina a fadin duniya, an tunatar da al’ummar Musulmi muhimmancin tabbatar da kiyaye naman hadaya da suke da shi a cikin tsafta.

Advertisement

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya baiyyana hakan a sakonsa na barka da Sallah da sashin hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ya fitar kuma ya turawa da Jaridar INDA RANKA.

Shugaba Tinubu yana son kokarin kirkiro da wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda kamar Boko-Haram a Arewa —Kwankwaso

Kwamishinan ya ba da shawarar cewa, dole ne a dafa naman yadda ya kamata sai kuma a soya shi, a ajiye shi a cikin waje mai tsafta, yana mai tabbatar da cewa ta yin hakan za a kare naman daga Cututtuka.

Advertisement

Dr. Labaran ya jaddada cewa, ya kamata mutane su guji cin naman da ya wuce kima da zafi domin yana iya cutar da ciki, ya kara da cewa duk wata alama da ke nuna rashin lafiya daga yanzu a kai rahoto ga cibiyar lafiya mafi kusa domin kula da lafiya.

Daga nan sai Kwamishinan ya bayyana gamsuwa da yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kyakkyawan aiki a cikin shekara guda duk da cikas da aka fuskanta, amma duk da haka ya a lgudanar da ayyuka da shirye-shirye masu kyau wanda hakan ke nuni da kasancewarsa mai bin tafarkin Dimokaradiyya na gaskiya.

Advertisement

“A madadin iyalaina da ma’aikata da hukumominta, ina taya Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da iyalansa, ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, shugabancin babbar jam’iyyar mu ta NNPP, taya murna na murnar Sallah. shugabancin karamar hukumar Gwale

 

Advertisement

“Ina kuma cikin kaskantar da kai na mika makamancin haka ga jagoranmu, shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, kuma jigo a tafiyar Kwankwasiyya, Mai girma Gwamna, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Allah Ya karbi dukkan ayyukanmu na sadaukarwa a matsayin aiki.na ibada.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending