News
Jami’an Yan Sanda Sun Kama Kansila Da Wasu Sarakunan Ƙauyuka Akan Satar Tiransifoma
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Jami’an Rundunar ‘Yan sanda sun kama kansila da wasu sarakunan kauyuka uku akan satar na’urar taransifoma a Jihar Gombe.
Premium Times ta ruwaito cewa Kakakin rundunar ‘yan Sandan Jihar Gombe Buhari Abdullahi ya gabatar da waɗanda ake zargin ranar Litinin.
An Dakatar Da Alkalan Kotu 4 Da Magatakarda Kan Wasu Laifuka A Kano
Wadan da ake zargi Kansilan Abdullahi Panda mai wakiltar Kumo ta Unguwar Gabas dake ƙaramar Hukumar Akko a Jihar Gombe.
Sauran wadanda ake zargin sun haɗa da Muhammad Majidadi mai shekara 40 wanda shi ne Hakimin Garin Majidadi, da Muhammed Sani mai shekara 43 wanda shi ne shugaban unguwar Sarkin Yaki da ke Kumo, da kuma Bello Ardo mai shekara 59 wanda shima yake rike da sarautar gargajiya.
Rahotanni na nuni da cewa A ranar 21 ga watan Yunin 2024 da misalin karfe 03:45 ne jami’an ‘yan Sanda daga yankin Akko suka kama waɗanda ake zargi da sace Tiransfomar kauyen Garin Majidadi wadda suka sayar wa Bello Ardo akan kuɗi naira Miliyan ɗaya da rabi 1.5.
Yace an ƙara kama sama da mutane 20 bisa zargin aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da kisan kai, da fashi da makami da sauran laifuka a Jihar.
Ya ce ‘yan Sanda za su ci gaba da bin diddigin masu aikata laifukan don hana cigaban ayyukan su a Jihar.
“Kwamishanan ‘yan Sandan Jihar CP Hayatu Usman ya buƙaci daukacin al’ummar Gombe masu son zaman lafiya da cigaban Jihar da su ba ‘yan Sanda haɗin kai, tare da kai rahoton duk wani motsi na mutane ga rundunar ‘yan Sanda mafi kusa a Jihar,” inji shi.
