Connect with us

News

Direban Tirelar Da Ya Kashe Mutum 14 A Masallacin Juma’a A Kano, Ya Tsere

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Aƙalla mutum 14 suka mutu, yayin da wata motar tirela ta ƙwace ta afka cikin masu halartar Sallar Juma’a a Jihar Kano.

Advertisement

Ibtila’in ya faru a garin Imawa, kusa da garin Kura, kan titin Kano zuwa Zariya.

Gwamnatin Tarayya Ta Karbi Ƴan Najeriya Kimanin 103 Da Aka Koro Daga Kasar Turkiyya

An ce tirelar mai lamba MKA 537 XN ta ƙwace wa direban, ta afka cikin masallatan.

Advertisement

An ce direban ya na kan hanyar Kaduna ne, yayin da yake ƙoƙarin ƙarasawa Kano, ya rage sauran kaɗan ya ƙarasa, hatsarin ya faru a garin Imawa, misalin ƙarfe 1:50 na rana.

Jami’an Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) daga Jihar Kano sun tabbatar da afkuwar mummunan hatsarin, kamar yadda Kwamandan Shiyya na Kano, Ibrahim Abdullahi ya tabbatar, ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran hukumar, Abdullahi Labaran.

Advertisement

Ya an rufe mutum 9 da rana bayan tashi daga Sallar Juma’a, yayin da waɗanda suka ji raunuka kuma na can ana kula da su a asibiti a jihar.

Premium Times ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun tabbatar da cewa direban da tuƙa tirela ɗin ya tsere, ganin irin mummunar ta’asar da ya aikata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending