News
Addu’ar Mutane Ce Ta Taimaka Wajan Kare Jihar Daga Bullar Cutar kwalara —Gwamnatin Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta dauki matakin kare al, ummar Jihar daga kamuwa da cutar kwalara.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a cikin shirin “Zauren Premier” na gidan rediyon Premier Kano.
Direban Tirelar Da Ya Kashe Mutum 14 A Masallacin Juma’a A Kano, Ya Tsere
Ya bayyana cewa, annobar cutar Kwalara ta bazu a jihohi 31 na Najeriya zuwa yanzu.
Ya cw Gwamnatin Kano ta kaddamar da wani shiri na wayar da kan jama’a musamman mazauna karkara yadda za su kare kansu.
Duk da cewa ba a samu bullar cutar kwalara a Kano ba, haka zalika ba a samu rahoton bullar cutar a kowace karamar hukuma ba,
Dr Labaran ya bayyana cewa gwamnati ta sayo magunguna domin yakar cutar idan ta bulla.
Haka zalika danganta halin da jihar ke ciki ba tare da cutar kwalara a Matsayin albarkacin addu’o’in al’ummarta.
Dr Labaran yace Addu’ar Mutane Ce Ta Taimaka Wajan Kare Jihar Daga Annobar Cutar kwalara
A matsayinmu na gwamnati, mun dauki matakan da suka dace, wadanda suka hada da sanar da kwamitinmu na Agajin Gaggawa (EPR) makonni biyu da suka wuce lokacin da cutar ta bulla a jihar Legas.”
“Kwamitin, wanda ya kunshi ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an sa ido da kuma malaman kiwon lafiya, da masu aikin sa kai na unguwanni, an dora wa alhakin bayar da rahoton duk wata bakuwar cuta ko annoba tare da daukar matakan gaggawa don dakile yaduwar ta,” in ji shi.
Ya kuma ce sun nada Asibitin Zana a matsayin cibiyar kula da wadanda ake zargin sun kamu da cutar Kwalara. Bugu da kari, sun fara gangamin wayar da kan masu siyar da abinci da masu siyar da ‘ya’yan itace don tabbatar da cewa sun kula da ayyukan tsafta.
Kwamishinan lafiya ya bukaci al’umma da su ba da hadin kai wajen dakile barkewar cutar ta hanyar kula da tsaftar muhalli da kuma nisantar bayan gida a fili.
