News
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf Yayi Allah Wadai Da Masu Safarar Kwayoyi A Jihar
DAGA ABDU ADO K/NAISA
Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ce zasu dauki mataki tare da saka kafar wando da su safarar kwayoyi
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa Gwamnan ya baiyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai Hukumar da ke kola da zarga zargr ababan ta jihar Kano KAROTA.
Addu’ar Mutane Ce Ta Taimaka Wajan Kare Jihar Daga Bullar Cutar kwalara —Gwamnatin Kano
Gwamnan Jihar Kano ya yaba da irin kokarin da hukumar ke gudanarwa bayan duba kayan aiki na manyan motoci da kuma irin kayayyakin da hukumar ta kama na kwayoyi da kayan maye.
Haka zalika yayi Allah Wadai da wadanda ya kira marasa kishin jihar Kano, wadanda suke taimakawa masu Harkar kwayoyi wajan tsaya musu don basu kariya.
Ya kara da cewar abin takaici ne hukuma ta kama kayan laifi! Amma wasu suyi kwance-kwance su karbi court order don dakile ayyukan gwmnati.
Abba Kabir yace zamu dauki mataki tare da saka kafar wando tsala don maganin masu irin wannan dabi’a
Gwamnan ya ja hankalin jami an hukumar da su kara jajircewa da yin aikinsu cikin tsari da doka domin magance bata gari a duk inda suke.
