Connect with us

News

Mu rika yiwa Kasa addu,a a duk farkon shekarar musulunci – Hon Yahya Abdullahi

Published

on

 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Advertisement

 

Dan takarar Shugabancin karamar Hukumar Burni da kewaye wato Kano Municipal a Jamiyyar New Nigerian People Party NNPP Hon Yahya Abdullahi Wanda akafisani da Baba Mai Duniya yana farin cikin mika sakon taya murna ga daukacin al’ummar Kano dangane da samun nasarar kammala shekarar Musulunci ta 1445 da kuma shiga shekarar 1446 ta hijirar

Advertisement

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa a sakon da Baba Mai Duniya ya kuma taya Jagoran Darikar Kwankwasiyya Dr Rabiu Musa kwankwaso dashi da  Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa comrade Abdussalam Gwarzo  da Kuma Shugaban ma,aikatan  fadar gwamnatin Jahar Kano shehu wada sagagi murna shigowar sabuwar shekara ta Hijiriyya tare dayin addu,ar fatan zaman lafiya da kwanciyar hankalin da dukkan Al,ummar musulmin duniya

Sannan Kuma ya yabawa Al, ummar kamar Hukumar Burni da kewaye wato Kano municipal na irin gudunmawar da Nuna soyayya da sukeyi masa a koda yaushe tare dayimasa adduar, samun nasara a kowanne lokacin wajen ganin ya samu nasarar a takarar sa

Advertisement

Ya Kuma bukai Jamia,n Tsaro dasu Kara jajircewa wajen ganin sun tabbatar da zaman lafiyar da kare kukiyoyin Al, umma

 

Advertisement

Ina kira ga Musulmin Najeriya da na duniya gaba daya mu yi addu’a Allah Ya ba mu lafiya da zama lafiya.

Duk inda Musulmi suke kuma Allah Ya taimake mu sannan mu rika mutunta addini.

Advertisement

Addinin Musulunci addini ne na tsoron Allah da zama lafiya, sunansa ma Islam, shi kuma Kirista addininsa addini ne na tausayi da mai addinin tausayi da mai addinin zama lafiya ai bai kamata suna fada ba, kai mai tausayi za ka zauna lafiya da kowa ballantana mai zaman lafiya, kai mai zama lafiya za ka zauna lafiya da kowa ma ballantana mai tausayi. A daina zuga mutane suna kashe junansu don biyan bukatar wasu ‘yan tsirarun mutante

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending