News
An Gudanar Da Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa Da Rashin Tsaro Da Lalacewar Tattalin Arziki A Kano
DAGA SALIM MUHAMMAD AHMAD
A safiyar yau ne gamayyar kungiyoyin matasa na cigaban alumma dake garin Chiranci Karamar Hukumar Kumbotso suka gudanar da tattaki hadi da addu’a a garin chiranci.
Matasan sun Fito cikin tsari dauke da kwalaye masu rubutu ma banbanta inda suke dagawa suna cewa bamu yarda ba bazamu yarda ba da auren jinsi, tsadar rayuwa, rashin tsaro da lalacewar tattalin arziki.
Ba za mu tafi yajin aiki ba idan muka cimma matsaya da gwamnatin Tarayya – Kungiyar ASUU
Gamayyar matasan sun gargadi wakilan su dake majalisar tarraya Sanata da da Majalisar wakilai da cewa kada su yarda su sahalewa wannan dokar, kusani mu kuke wakilta, kuma mu musulmai ne don haka wajibi ne ku kare mana hakkin mu.
Muna kira ga maigirma Gwamnan Kano, Gwamnan al’umma daya barranta jihar kano da yadda da wannan tsarin, muna rokon malaman mu da su cigaba da watsi da wannan alamari, muna bukatar Yan majalisun mu su yi sani cewa wayanda suke wakilta fa suna cikin kuncin rayuwa, ba tallafi ake bukata ba, ana neman chanji me dorewa don haka ayi duk abunda za ai a nemawa talaka saukin rayuwa.
Bluelens Multimedia
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
