Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata jawabin ‘Tinubu Speaks’ da ke yawo

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A wani yunƙurin gaggawa game da wani jawabi da aka yi wa laƙabi da ‘Tinubu Speaks’ da ake danganta shi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata abin da ke ciki tare da nesanta Shugaban da shi.

Advertisement

A ranar Asabar ne Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya yi watsi da saƙon, yana mai cewa ba gaskiya ne abin da ake jingina wa Shugaba Tinubu.

Muhimmancin Danyen Mai A Fannin Tattalin Arzikin Duniya Da Kuma Matsayin Kasancewar Matatar Mai Ta Dangote A Kasuwar Mai Ta Duniya —Dr Abbati Bako

Ana yaɗa ƙirƙirarren labarin ne a kafafen sada zumunta kan cewa wani jawabi ne da Tinubu ya yi inda ya ke magana game da ƙalubalen da tattalin arziƙin Nijeriya ke fuskanta.

Advertisement

Jawabin ya kunshi batutuwa da suka haɗa da; batun rage albashin manyan ma’aikata da kashi 50, rushe ofishin matar shugaban ƙasa, dawo da tallafin mai da na wutar lantarki a matsayin yunƙurin gwamnatin na daidaita al’amuran ƙasa.

Ƙirƙirarren zancen, ya kuma ƙunshi cewa shugaban ƙasa na shirin rage adadin ministoci, sayar da jirgin ofishin shugaban ƙasa da kuma dakatar da fita ƙasar waje domin duba lafiya ga ma’aikatan gwamnati.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending