News
‘Yan Sanda Sun Kama Mutum 3 Da Ake Zargin Su Da Kashe Abokinsu A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce wani mazaunin unguwar Dorayi Kwatas ya kai ma ta rahoton bacewar wani dan uwan shi mai suna Dahiru Musa mai shekara 32, kuma su na zargin daya daga cikin abokan shi da hannu a batan shi.
Hakan na kunshe cikin sanarwar da rundunar ‘yan sanda ta aikewa manema labarai, inda a kayi nasarar kamo wanda ake zargin mai suna Aliyu Adamu tare da fara bincike kan lamarin.
Matukin Jirgin Saman Ya Mutu Ana Tsaka Da Sharara Gudu A Sararin Samaniya
A karshe ‘yan sandan sun gano an kara haduwa da wani abokin na daban mai suna Mubarak Abdulsalam, inda suka rankaya unguwar Gaida da nufin tattaunawa kan harkar kasuwanci. Anan ne aka bai wa Dahiru abinci dauke da guba, bayan ya fita hayyacinsa ne suka yi daba ma sa wuka har sai da ya mutu.
Samun labarin kama Aliyu da ‘yan sanda suka yi, ya sanya Mubarak kiran wani abokin na shi suka hadu tare suka zubawa gawar Dahiru man fetur tare da kone ta, sannan suka tattara abin da ya yi saura a leda da jefawa a wani kango.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba ne ya yi holen wadanda aka ake zargi da kisan Dahiru, ya yi kiran ya mutane su dinga taka tsantsan kan mutanen da suke mu’amala da su da abokan huldar ksuwanci, da kaucewa amsa gayyata zuwa wani wuri kebantacce da ya kaucewa idanun jama’a.
