Connect with us

News

Yadda Al’ummar Kano Suka  Ƙara Shiga Cikin Mawuyacin Hali Saboda Matsalar Wutar Lantarki

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Faɗuwar babban layi wutar lantarki na jihohin Arewa ya jefa jjhohin cikin matsanancin hali, inda al’umma a Kano suka fara kokawa saboda tsayarwar komai waje guda da kuma fama da duhu da suke yi da daddare.

A halin yanzu dai da yawan kasuwanci da suka dogara da wutar lantarkin sun tsaya cak a yayin da ake cigaba da fuskantar tsadar man fetur.

Iya Mummunar Addu’ar Ku, Da Mummunan Fatan Ku Ga Najeriya Iya Kara Lalacewar Kasar Da Kara Lalacewar Shugabannin ku

A baya dai a irin wannan yanayi al’umma kan koma ne su rugumi injinan ganerata, amma tsadar man fetur ya sanya su cikin tsaka mai wuya, gaba kura baya sayaki.

Advertisement

Haka zalika da yawan ‘yan kasuwa kan zauna a shagunansu cikin tsafi da ƙunci wanda ya hakan ke tilasta musu yin ciniki daga wajen shago saboda a sha iska.

A gidaje kuwa abin ba a cewa komai, domin binciken Premium Times ya nuna yadda wasu iyalan suka fara yin asarar kayan abincin da sukan ajiye a firij (freezer) – kama daga kayan miya da nama da kayan marmari da makamantansu da tuni suka fara ruɓewa.

Idan kuwa ana maganar ruwan sanyi a yayin da ake tsala matsananciyar rana, to fa abin ba sauƙi domin rashin wutar ya sanya ana fama da ƙarancin ruwan sanyi kuma ko da masu sayar da ruwan ba safai ya cika yi sanyin da zai gamsar ba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *