Connect with us

News

Iya Mummunar Addu’ar Ku, Da Mummunan Fatan Ku Ga Najeriya Iya Kara Lalacewar Kasar Da Kara Lalacewar Shugabannin ku

Published

on

Iya Mummunar Addu'ar Ku, Da Mummunan Fatan Ku Ga Najeriya Iya Kara Lalacewar Kasar Da Kara Lalacewar Shugabannin ku

 

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Advertisement

 

Assalamu alaikum

Advertisement

A yau, duk mai bibiyar kafafen yada labarai na yanar gizo da wadanda ma basu ba. Ko kuma idan ka bibiyi wurin zama da majalisun ‘yan Najeriya da wuraren firar su, zaka tarar da wasu abubuwan ban mamaki. Wato irin yadda al’ummah suka koma basu komai sai kokarin yin batanci ga kasar su, kasar da basu da wata kasa da ta wuce ta. Ko kuma ka same su suna zagi, ko cin mutunci, ko wulakanci, ko la’ana da tsinuwa ga shugabannin su, duk da sunan wayewa ko kuma da sunan siyasa, ko ci gaba.

Ta wannan hanya, sai aka wayi gari kullun, babu abunda muke yi sai kara jefa kasar mu cikin damuwa daban-daban da bakunan mu.

Advertisement

CDE, KANSIEC Sun Shirya Taron Masu Ruwa Da Tsaki Akan Zaben Kananan Hukumomi

Kai wasu ma har wasu sunaye na shakiyanci suke kirkirowa, suna jifar shugabannin su dasu. Kamar yadda suka sanya wa shugaban kasar Najeriya, wato Bola Ahmed Tinubu wani suna wai shi T-Pain, ma’ana, yana nuna wai ana shan wahala, ko kuma Tinubu ya kawo wahala, duk da sunan wayewa.

‘Yan uwana masu girma, ku sani, ko shakka babu, kyakkyawar addu’a ga kasar mu da shugabannin mu, da kyakkyawan fata a gare su, shine mafi alheri a gare mu, kuma yana daga cikin manyan hanyoyin da zamu bi domin neman Allah Subhanahu wa Ta’ala ya tausaya muna, ya dafa zukatan shugabannin namu, ko kuma ya kawo muna abunda yake shine mafi alkhairi a gare mu.

Advertisement

Ku sani, ayyana mummunan fata ga kasar mu mai albarka Najeriya, ko zagi ko tsinuwa ko la’antar kasar ko shugabanninta, wallahi ba yadda za’a yi ya zama hanyar samun sauki akan wahalhalun da muke ciki. Maimakon ma a samu sauki, matukar bamu daina zagin shugabanni ba, matukar bamu daina zagin su ba, matukar bamu koma muna yiwa kasar mu addu’a da fatan alkhairi ba, to a gaskiya wahala sai dai abun da ya karu. Allah ya sawwake, amin!

Ko shakka babu, tabbas, hakika, kasar nan ana cikin wani irin yanayi marar kyau kuma marar dadi. Babu mai musu ko jayayya akan haka. Ko su shugabannin sun sha fada cewa, sun san ana shan wahala. Abinci ya gagari talakawan Najeriya. Kunci da damuwar rashin tsaro da rashin tabbas, duk sun addabi al’ummah. Babu mai shakka akan wannan.

Advertisement

To amma, a inda gizo yake sakar shine, mu tambayi kawunan mu, shin tsakanin mu da Allah Mahaliccin mu, mafita game da wannan matsala ita ce, mu koma muna yin batanci ga kasar mu? Kokuma mu koma muna zagi, ko tsinuwa ko la’antar shugabannin mu?

Duk wani mai hankali, mai ilimi, mai basirah da hangen nesa, yasan cewa ba anan mafitar ta ke ba.

Advertisement

Ku sani, a duk lokacin da kuke batanci ga kasar ku, to kara lalacewa take yi. A duk lokacin da kuke zagi ko la’anta ko tsinuwa ga kasar ku da shugabannin ku, wallahi kara samun matsala suke yi. Ko sun zo da nufin alkhairi, sai Allah ya canza su, su zamar muna bala’i, sanadiyyar miyagun kalaman da suke fita daga bakunan mu.

Maimakon shugabannin su gyaru, muji dadin su, kun ga sai kuna kara bayar da gudummawa kenan, wurin kara lalacewar kasar da shugabannin ta.

Advertisement

Duk wanda ya karanci addinin Musulunci kuma ya fahimce shi, fahimta ingantacciya, to yasan wannan maganar haka take, ko shakka babu. Duk abunda ake zagi, ko menene shi. Ko kuma ake la’antar sa ko tsine masa, to babu yadda za’a yi wannan abun yayi kyawo ko yayi albarka. Allah cire albarka yake yi, cire arziki yake yi ga duk abunda ake zagi ko la’antar sa.

Shi yasa har kullun, kasar mu Najeriya mai albarka, mai dimbin arzuka iri-iri, daban-daban. Kasa mai cike da dimbin masana, masu ilimi ko wane iri. Kasa mai cike da tarin al’ummah. Kasar da duniya ta shaida cewa jagora ce ga wasu kasashen duniya masu yawa, amma an wayi gari duk mun lalata kasar da ayukkan mu marasa kyawo. Mun bata kasar da bakunan mu. Mun tsine mata, mun la’ance ta. Mun tsine wa shugabannin mu, mun kasance muna la’antar su da zagin su, hakan sai ya bayu zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala ya cire albarkar sa ga kasar. Wal iyazubillah!

Advertisement

An wayi gari kasa ta zama, GA KOSHI GA KWANAN YUNWA!

 

Advertisement

Allah ya sawwake, amin.

‘Yan uwana masu girma! Abu Zaid Thabit Bin Dahhak Al-Ansari, Allah ya kara masa yarda, yace: Manzon Allah (SAW) yace: “…La’antar Musulmi ko zagin sa, kamar kisan sa ne.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi]

Advertisement

Abu Hurairah, Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah (SAW) yace: “Ba ya dacewa ga mumini mutumin kirki ya zamo mai zagi ko la’antar mutane.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

Abu Ad-Darda Allah ya kara masa yarda yace: Manzon Allah (SAW) yace: “Masu zagi ko la’antar mutane ba’a karbar shedar su, kuma ba za’a sa su cikin masu ceto ba a ranar alkiyama.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

Advertisement

Samurah Bin Jundub Allah ya kara masa yarda yace: Manzon Allah (SAW) yace, “Kar ku zagi juna ko ku la’anci juna, ko ku tsinewa juna, yin hakan zai iya jawo maku la’antar Allah da fushin sa ko azabar wutar jahannama.” [Abu Dawud da Tirmizi ne suka ruwaito shi]

Ibn Mas’ud Allah ya kara masa yarda yace: Manzon Allah (SAW) yace, “Ba zaka taba samun mumini na gaskiya a cikin harkar wulakanta wani ko cin mutuncin wani, ko zagi, ko tsinuwa ko la’anta ba.” [Tirmizi ne ya ruwaito shi]

Advertisement

Abu Ad-Darda Allah ya kara masa yarda yace: Manzon Allah (SAW) yace, “A duk lokacin da mutum ya zagi wani mutum, ko ya zagi wani abu, ko ya la’ance shi ko ya tsine masa, to a lokacin tsinuwar za ta tafi sama, za ta tarar da kofofin sama a rufe. Sannan tsinuwar za ta dawo kasa, ta tarar da kofofin kasa a kulle. Daga nan wannan tsinuwa za ta yi dama tayi hagu tana neman wurin da za ta sauka, idan ba ta samu wurin sauka ba sai ta dawo kan wanda aka tsine wa, idan ta dawo kan sa, to anan idan ya cancanci tsinuwar sai ta fada masa, idan kuma hai cancanci tsinuwar ba, to sai ta dawo kan wanda yayi ta, ta halaka shi, ta lalata rayuwar sa, yaki yin albarka.” [Abu Dawuda ne ya ruwaito shi]

Imran Bin Husain Allah ya kara masa yarda yace: wata rana muna cikin halin tafiya tare da Manzon Allah (SAW), kuma a cikin mu akwai wata mata mutuniyar Madinah tana saman taguwar ta. Sai wannan taguwa ta wannan mata ta dan yi gardama wurin tafiya, sai matar ta zagi wannan taguwa kuma ta tsine mata, ta la’ance ta. Da Manzon Allah (SAW) yaji wannan mata, nan take sai yace, “ku sauke kayan wannan taguwa, ba zamu yi tafiya da ita ba, ku kora ta ta shiga daji, saboda an tsine mata, idan ba haka ba tsinuwar da la’antar zasu shafe mu.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

Advertisement

 

Abu Barzah Nadlah Bin Ubaid Al-Aslami Allah ya kara masa yarda yace: wata rana wata mace tana tafiya akan taguwa, a cikin yanayin tafiya. Kuma taguwar wannan mata tana dauke da kayan mutane. Kawai sai ta ga Manzon Allah (SAW). Sai hanyar tayi mata kadan, don haka sai ta kasa wucewa. Matar tayi ta kokarin wannan taguwa ta wuce taki wucewa, sai kawai tace Allah ya tsinewa wannan taguwa. Kawai sai Annabi (SAW) yace, “Ku cire wannan taguwar da aka la’anta daga cikin mu. Ba zata yi tafiya tare da mu ba.” [Muslim ne ya ruwaito shi]

Advertisement

 

Jama’ah ku dubi irin yadda wadannan Hadisai na Manzon Allah (SAW) suka karantar da mu hadarin la’anta, ko zagi ko tsinewa wani mutum ko wani abu. Kuma mun ga irin yadda Annabi (SAW) da kan sa, ya karantar da mu cewa, lallai idan muna zagin wani abu ko la’antar sa ko tsine masa, to zai lalace, kuma ba zai taba yin albarka ba. Kuma wannan zai sa mu kara shiga wahala da damuwa a rayuwar mu. Don haka wallahi ya zama dole, tilas kuma wajibi mu kiyaye harsunan mu.

Advertisement

 

Misali, ko mahaifi ne yake zagin dan sa, ko yake tsine masa ko la’antar sa, to ba zai taba yin albarka ba!

Advertisement

 

Kuma bamu ce ba’a shan wahala a kasar nan ba. Kuma bamu ce shugabannin basu yin kuskure ba. Su mutane ne kamar kowa, suna iya yin daidai, kuma suna iya yin kuskure. Amma abun da muke cewa shine, tun da mafita da gyara ake nema ga kasar na, to yana daga cikin hanyoyin samun gyaran shine, mu kiyayi harsunan mu, mu daina yin batanci ga kasar mu mai albarka. Mu daina zagi, ko cin mutunci, ko la’anta, ko tsinewa shugabannin mu. Maimakon haka, mu yiwa kasar mu da shugabannin mu addu’o’i masu kyau. Muyi wa kasar mu da shugabannin mu fatan alkhairi. Mu kauce wa duk wata hanya da zata jawo kara lalacewar su!

Advertisement

 

Sannan daga karshe, ku kuma shugabanni kuji tsoron Allah. Ku sani, kasar nan ana cikin matukar damuwa ba kadan ba. Don haka ya zama dole, tilas kuma wajibi a gare ku, ku bi duk wata hanya, wadda zata samar da sauki ga dukkanin ‘yan kasa. Kuma ku kauce wa bin duk wata hanya wadda zata kara jawo sanadiyyar tsanantawa ‘yan kasa.

Advertisement

 

Allah yasa mu gane, amin.

Advertisement

 

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a wannan lambar waya kamar haka: 08038289761.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending