Connect with us

News

Muddin Gwamnatin Tarayya Bata Sauya Tunani Ba, Baza A Samu Sauyi Mai Inganci Ba Nan Da Shekaru 15 —Dr Abbati 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA

Babban mataimakin shugaban bankin Duniya Mista Indermit Gill ya ce za’a samu sauye sauye masu amfani a fannin tattalin arzikin Najeriya nan da Shekaru 10 zuwa Shekaru 15 masu zuwa.

Advertisement

Mista indermit ya bayyana hakan ne a wani taro da Kungiyar Kare tattalin arziki Najeriya tayi tare da tallafin Ma’aikatar Kasafin Kuɗi da tsare tsare ta Najeriya tayi Karo na 30 a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Yadda Al’ummar Kano Suka  Ƙara Shiga Cikin Mawuyacin Hali Saboda Matsalar Wutar Lantarki

Amman saidai a nazari da Kuma zurfin tunani da Dr Abbati Bako yayi ya gano cewar koda nan da Shekaru 15 za’ayi baza’a taba samun sauyi mai Inganci ba muddin idan har gwamnati ɓata sauya tunanintaba a wasu mahimman bangarori da suka shafi Kasar .

Advertisement

Dr Abbati Bako ya ce a Nijeriya tana fama da Kusan Muta ne Sama da MilIyan 130 da basa iya cin Abinci a kowacce Rana Kuma hanyoyin da gwamnatin Bola Tinubu take bi ba hanyoyin bane da za’a Sami sauki da cigaba kasa nan da Shekaru 15 da gwamnatin take ikirari ba.

Najeriya na fama rashin cigaba a fannin tattalin arziki da rashin ci gaba a fannin kiwan lafiya wanda a halin yanzu Najeriya ke kai al’ummar su cikin rukunin kulawar gaggawa na (ICU) ba tare da lokacin lokacin mutuwarsu yayi ba.

Advertisement

Dr Abbati Bako ya cigaba da cewa a halin yanzu, Najeriya ita ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Kasashen Afirka amman kuma tana cikin tsaka mai wuya ga Kuma tarin Albarkatu amman a haka wai ake ikirarin sai nan da Shekaru 15 za’a sami saukin rayuwa tom ai ni banga Wata alamar hakan ba inji shi.

Nageriya tana da karfin tattalin arziki na ( GDP ) da darajarsa ta kai dala biliyan 511 a cewar bankin duniya( IMF) Wanda Kasashe 3 ne a Kasashen Afirka da suke da kwatankwacinsa irinsa da suka hadar da Africa ta Kudu da kuma Kasar Masar.

Advertisement

Al’ummar Najeriya na acikin maduwa matukar gaske game da cire tallafin Man fetur da kuma bukatar ko dai a cire shi na dindindin ko kuma a mayar da shi baya bisa bukatun ‘yan kasar.

Masana tattalin arziki da dama a siyasa sun bayyana damuwarsu dangane da cire tallafin man fetur a Najeriya, inda suka yi nuni da yadda wasu kasashe irin su Kenya, Mexico, Venezuela, Brazil da Afrika ta kudu suka gaza samun nasara, da sauran kasashen kudancin duniya da kuma tsohuwar Tarayyar Soviet dake gabashin kasar Turai.

Advertisement

A koda yaushe gwamnati tana saka Adalci a cikin lamuranta muddin tanason cigaban Al’ummarta da kuma gina goben Kasar.

Dr ya ce mu duba koda a baya bayannan irin halin da Kasar Bangladesh take ciki sanadiyyar cire tallafin mai Fetur Amman a haka gwamnatin Najeriya tayi kunnen uwar shegu ta cire tallafin fetur duk kuwa da shawarwarin masana

Advertisement

Kasashe masu tasowa na fama da Kalubalen tsaro a cikin ƙasashe masu tasowa na Kudancin Duniya kuma hakan yasa suke bada gudummawa ga matsalolin tattalin arzikin Kasashe masu tasowa ciki harda Najeriya.

Dr ya ce kowacce Kasa indai har anaso ta sami cigaba mai dorewa tom ya zama dole ta a sami zaman lafiya da karfin tattalin arziki na gaske.

Advertisement

Babban mai ba da shawara na Bankin Duniya (IMF ) kuma masani a Washington Consensus kan sauye-sauyen tattalin arziki a kasuwanni masu tasowa na tattalin arziki Farfesa John Williamson ya yi shiru baice uffan ba kan sauye-sauyen na dogon lokaci da Najeriya ke ikirarin yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana matukar kokari game da tunkarar kalubalen tsaro, musamman ma ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Advertisement

‘Yan kasar na neman amsoshi da tsare-tsare daga Majalisar Dinkin Duniya, tare da jaddada mahimmancin shigar da suke da shi wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya tare da danganta ci gaban tattalin arziki da ci gaban kasashe masu tasowa na tattalin arziki na duniya.

Duk da dimbin albarkatun kasa da dama da kasar ke da shi, kasar na fuskantar matsanancin rashin tsaro da rashin tattalin arziki, da durkushewar masana’antu ga wahalhalu ga rashin taka tsantsan a wajen gwamnati

Advertisement

 

Dr ya Kara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bullo da sauye-sauye a fannin tattalin arziki tom amma ba a da tabbas kan tasirinsu yayin da Najeriya ke tukarar zaben shekarar zabe ta 2027.

Advertisement

tasirin wadannan sauye-sauye da Bankin Duniya da IMF, kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya, da kwanciyar hankali, da ci gaban kasar kamar yadda yake faruwa a kusan dukkanin Kudancin duniya. Wannan rubutun yana kan shafi daya ne da Dakta NgoziOkonjo-Iweala babbar daraktar kungiyar kasuwanci ta duniya (WTO) a taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA).

Ngozi Okonjo-Iweala ta ce Najeriya ɓata sami cigaban da ake bukataba a fannoni Daban daban daban na tsarin Yan kasar ba.

Advertisement

 

Haka zalika babbar daraktar kungiyar ta WTO, ta bayyana damuwarta game da rashin ci gaban Najeriya, inda ta bayyana matukar damuwarta .

Advertisement

MATSALOLIN NAJERIYA

1 Rashin manufofin ayyukan gudanarwa.

Advertisement

2. Rashin abubuwan more rayuwa ga Yan Kasa.

3 Baiwa Yan kwangila manyan ayyuka kuma Basu chanchantaba.

Advertisement

4 An siyasantar da harkar tsaron Al’umma ta hanyar baiwa wadanda Basu daceba mukaman shuwagabannin tsaro sabida sunyi hidima lokacin yakin neman zabe.

5 Hauhawar farashin kayayyaki.

Advertisement

6 Rashin aikin yi.

7 Dogaro da shigo da tataccen Man Fetur daga Kasashen waje duk kuwa da cewa akwai Allah ya azurta Kasar da Man Fetur Kuma akwai matatatu Amman basa aiki sabida san zuciyar shuwagabannin.

Advertisement

8 Cin hanci da rashawa

9 Rashin kulawa yaddda ya kamata a fannin noma.

Advertisement

10 rashin hanyoyin magance kalubalen tsaro.

RASHIN HANYOYIN BUNKASAR TATTALIN ARZIKI GA TSARIN SHUGABANCIN TINUBU .

Advertisement

1 Rashin tabbatar da ingancin ayyuka.

2 cire hannu daga kamfanunawa mallakin gwamnati.

Advertisement

3 Faduwar darajar kuɗin naira.

4 Zuba jari a kayayyakin more rayuwa

Advertisement

6. Cire duk tallafi

7. Rashin magance tabarbarewar tattalin arziki a kasar nan.

Advertisement

 

TSARUKAN BANKIN DUNIYA

Advertisement

1. Shirye-shiryen Daidaita Tsari (SAPs)

2 Lamunin daidaita tattalin arziki

Advertisement

3. Shawarar ta manufofi da taimakon fasaha

SHAWARAR DR ABBATI BAKO KAN INGANTA MANUFOFIN TATTALIN ARZIKI

Advertisement

 

 

Advertisement

Yayin da sauye-sauyen Shugaban Tinubu ya kamata ya gane rashin biyewa shawarwarin (IMF) zaifi alkhairi akan biyemusu

1 dakarun kawo cigaba da habaka tattalin arziki

Advertisement

2 baiwa masu kananan karfi jari

3 Shawarwarin masana Yan Kasa

Advertisement

4 tayar da masana’antu

5 dakile cin hanci da rashawa

Advertisement

6 baiwa fagen zamani kyakkyawan tsari

7 Ƙarfafa zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje (FDI) daga dukkan ƙasashen duniya

Advertisement

8 Haɗin gwiwar tattalin arziki na yanki; musamman a yankin yammacin Afirka

9 Bunkasa fannin noma

Advertisement

SHAWARAR KARSHE

gyare-gyaren tattalin arziki na Shugaba Tinubu da na Bankin Duniya/IMF dole ne a yi nazari a tsanake don tabbatar da inganta ci gaban tattalin arziki mai dorewa, kwanciyar hankali, tsaro da kuma tsara dabarun ci gaban hanyoyin sufurin jiragen kasa a Najeriya don gaggauta bunkasar tattalin arziki da ci gaba. Kuma daidaitaccen tsarin kula da duk hanyoyin da aka ambata a sama-ASAP.

Advertisement

Dr. Abbati Bako mai bada da shawara kan dabarun siyasa da sadarwa kuma ma’ajin kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano, Nigeria.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending