Connect with us

News

Babu Ranar Samun Wutar Lantarki A Yankin Arewa – Hukumar TCN

Published

on

Babu ranar samun wutar lantarki a yankin Arewa Hukumar TCN

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar wutar lantarki ta ƙasa ta bayyana cewa matsalar da aka samu na lalacewa wutar layukan samar da wutar lantarki a yankin Arewacin Najeriya ne ya sa yankin kaf ɗinsa ya afka cikin ƙungurmin duhu.

A wata sanarwa da Kakakin hukumar TCN ta fotar ranar Talata, ta ce tun da karfe 4 na asuban ranar Litinin, aka samu matsala da ya yi sanadiyyar lalacewar wutar lantarki.

Kotu Ta Rushe Shugabannin Hukumar Zaben Kano Kwanaki 4 Gabanin Zaben Kananun Hukumomin Jihar.

” Mbah ta ce da misalin karfe 4:53 na safiyar ranar Litinin, Layin Ugwuaji–Markurdi 330kV 2 ya lalace sannan sai aka ɗauke wuta 243 MW akan wannan layin aka maida shi zuwa Layi 1 akan wannan hanya.

 

“Haka duka layukan duk suka katse, babu wuta akan su kuma ba mu san inda wayoyin suka samu matsala ba.

Advertisement

 

” Mun tura injiniyoyin mu su fantsama cikin dazuka, ƙoramu da tsaunka tun daga Enugu zuwa Makurɗi tare da jami’an tsaro domin a bi a duba ina aka samu matsalar.

” Wasu ma’aikata sun fara aiki tun jiya, daga Makurɗi amma har cikin dare ba su cimma inda matsalar take ba. Sannan daga Enugu kuma injiniyoyi ba su iya soma aiki ba saboda dokar hana fita da ƴan kungiyar IPOB suka saka a wannan rana a duk yankin jihohin Igbo.

Mba ta ce a yau Talata ne za a cigaba da laluben har sai an kai ga ganin inda matsalar take.

A ƙarshe tace an samu matsala kuma a tashar samar da wutar lantarki da ke Mando. Gaba ɗaya ya durkushe. Shima kuma ya yi sanadiyyar rashin samun wuta a wasu sassan yankin Arewa.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending