News
Abuja Za Su Fuskanci Katsewar Wutar Lantarki Na Kwana 16 –Kamfanin AEDC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A ranar Juma’a, kamfanin rarraba wutar lantari na babban birnin tarayya Abuja (AEDC) ya bayyana cewa akwai yuwuwar katsewar wutar lantarki daga ranar 6-12 ga watan Janairun 2025 a wasu sassa na Abuja.
Kamfanin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X a ranar Juma’a.
Yan Sanda Sun Kama Matashi Da Laifin Garkuwa Da Ɗan Shekara 2 A Kano
Ya ce, za a samu katsewar wutar ne sakamakon gyara da hukumar raya birnin tarayya za ta yi na musayar Na’urar ba da wuta mai yawan 33KV da ke ba wa filin jirgi wuta da kuma babban layin wuta mai girman 132KV na Kukwaba-Apo da ke babban hanyar da ta yi Kudu da Abuja.
A cewar sanarwar, wuraren da wannan abu zai shafa sun haɗa da: Lugbe da kewayenta da titin filin jirgin sama da Kapwa da NNPC da Games Village, da babban filin wasa na ƙasa da asibitin ido da rufaffen filin wasa da cojin Christ Embassy da makaranta mai suna American International School da Spring Court, rukunin gidajen jakadancin Amurka da American Embassy Quarters da shalkwatar hukumar EFCC da Coca Cola da tashar jirgin sama da asibitin gwamnatin tarayya na FMC.
Sauran wuraren sun haɗa da wani ɓangare na Apo, da wasu ɓangarori na Gudu da Gbazango da kewayanta da wani ɓangare na Kubwa da Bwari da kewayanta da wani ɓangare na Jahi da wani ɓangare na Jabi da Karu da Nyanya da Mararaba da Keffi da kewayanta da sauran wasu ɓangarori da ke Abuja.
“Muna masu ba ku haƙuri da jin daɗin yadda kuka fahimci wannan tsaiko da za a ɗan samu,” in ji sanarwar.
