Connect with us

News

Ya Kamata Dalibai Su Kara Zage Dantse Wajen Neman Ilimin  AL-KUR’ANI Me Girma .

Published

on

IMG 20250105 WA0013

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban Karamar Hukumar Madobi Alhaji Suleiman Dan Azimi ne ya yi wannan Kiran lokacin bikin saukar karatun al-kur’ani me girma na madarasatul imamu Ahmad bin hambali islamiyya kwankwaso kofar arewa.

Advertisement

Suleiman Dan Azimi Wanda ya Sami wakilcin me bashi shawara a harkar yada Labarai da wayar da Kan al-uma Honorabil Nasir Suleiman Nasir kwankwaso,ya Kara da cewa majalisar Karamar Hukumar a shiye take wajen ganin ta baiwa Ilimin Addini da na zamani fifikon da ya kamata Dan ganin Karamar Hukumar ta Samar da Hafizan Al-kur’ani me girma a Loko da sakonta.

Abuja Za Su Fuskanci Katsewar Wutar Lantarki Na Kwana 16  –Kamfanin AEDC

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwar da jami’ín yada labarai na Karamar Hukumar Madobi Auwalu Musa Yola  ya turawa da Jaridar INDA RANKA

Advertisement

Da Yake Jawabi tunda farko, Shugaban Makarantar Malam Liman M. Muhammadu ya ce an kafa Makarantar ne a Shekara ta 2011 a Matsuguninta na wucin gadi dake unguwar Rimi kofar Arewa .

Shugaban Makarantar ya Kuma Mika kokon bararsu ga mahukuntan game da sauran masu hannu da shuni da su duba yiwuwar samarwa da Makarantar Matsuguni na dun dun dun.

Advertisement

Shima anasa jawabin Shugaban kungiyar iyaye da Malamai na Makarantar Alhaji Sabiu Ibrahim Kwankwaso ya baiyana godiyarsa ga Allah SWT tare  baiyana Jin dadinsa ga iyaye da Malamai na Makarantar bisa gudunmawar da suka  bayar wajen ganin an Sami nasarar gudanar da saukar ta Dalibai 42 a Karo na Uku.

Alhaji Sabiu Ibrahim Kwankwaso ya Kuma roki  shugabancin Karamar Hukumar da sauran masu hannu da shuni dake Yankin da su gyarawa Makarantar ajin da suke aro sakamakon zuba da yake yi lokacin  damuna tare da samarwa daliban Makarantar Tsaftataccen ruwan Sha Dan gudanar da ibadar sallah duba da lalacewar da rijiyar Makarantar ta yi.

Advertisement

Manyan Malamai na Yankin sun fadakar da Dalibai game da mu’ujizojin al-kur’ani me girma Wanda suka hada da Alkali Yusif Kawu Madobi, da Gwani Dakta Aliyu Muhammad Murtala daga Kwalejin Sa’adatu Rimi Dake Kumbotso da Sauransu.

Wasu daga cikin Daliban da sukai saukar Hassan Usman Kwankwaso, da Maimunatu Muhammad Adam sun baiyana farin cikinsu a wannan Rana tare da godewa Iyayensu da Malamansu bisa gudunmawar da suka ba su ba dare ba Rana har wannan nasara ta tabbata.

Advertisement

A inda Uban Taro , Hakimin Madobi Majidadin Kano Alhaji Baba Musa Saleh Kwankwaso ya Mika Allunan Zaiyana ga daukacin Daliban tare da godewa duk wadanda suka bada gudunmawarsu wajen ganin an Sami wannan nasarar.

Daga nan ya bayar da tabbacin cewa , fadarsa zata zauna da mahukuntan wannan Makaranta da shugancin Karamar Hukumar wajen ganin yiwuwar samarwa da Makarantar Matsuguni na dun dun dun kamar yadda aka bukata nan bada jumawa ba.

Advertisement

An Karrama wasu daga cikin Al-umar garin na Kwankwaso wadanda suka bada gudunmawarsu wajen ci gaban Makarantar wasu na raye, wasu Kuma Allah ya karbi rayuwarsu.

Gwani Malam Sani Abdulsalam Kwankwaso,  Kuma kwamandan Hisba na Karamar Hukumar Madobi shi ne ya jagoranci yiwa Daliban Darasu.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending