Connect with us

Sports

An kawo karshen Man City bayan wasa 32 a jere ba tare da anyi nasara akanta ba

Published

on

IMG 20241103 WA0026
Spread the love

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO

Manchester City ta yi rashin nasara daci 2-1 a gidan Bournemouth a wasan mako na 10 a Premier League da suka fafata ranar Asabar a Vitality.

Minti tara da fara tamaula Semenyo ya fara zurawa Bournemouth ƙwallo, kuma haka suka je hutun rabun lakaci ba tare d an kara kwallo a ragar kowa ba.

Advertisement

Robert Lewandowski ya lashe kyautar ‘dan wasan da ya fi bajinta a La Liga na watan Oktoba

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne, Bournemouth ta kara ta biyu ta hannun Evanilson daga baya City ta zare ɗaya ta hannun Gvardiol, saura minti takwas a tashi wasan.

Kenan Josko Gvardiol ya ci ƙwallo ta shida a wasan waje daga bakwai a Premier League.

Da wannan sakamakon Bournemouth ta kawo karshen Man City a wasa 32 a jere a lik ba tare da rashin nasara ba a babbar gasar tamaula ta Ingila.

Advertisement

City mai rike da Premier League ta ci karawa 26 daga ciki da canjaras shida, wadda rabon da ta yi rashin nasara a lik tun 1-0 a hannun Aston Villa ranar 6 ga watan Disamba.

Wannan shi ne karon farko da City ta buga karawa a waje ranar Asabar da karfe huɗu agogon Najeriya, tun bayan rashin nasara a Wolves a Satumbar 2023.

Erling Haaland wanda bai zura ƙwallo ba a ranar ta Asabar ya ci 74 a wasa 75 a Premier League, tun bayan da ya koma Etihad.

Advertisement

Saura ƙwallo ɗaya yayi kan-kan-kan da Alan Shearer mai 75 a karawa 93 a matakin wanda ya ci da yawa a gasar ta firimiyar kasar ingila.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *