News
Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hezbollah Ta Fara Aiki A Lebanon
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A yayin da tsagaita wutar ta fara aiki, anga jerin motoci sun nufi kudancin Lebanon, inda aka shafe watanni ana gwabza kazamin fada da kuma umarnin Isra’ila na tilastawa mutane barin gidajensu.
Sojojin Isra’ila sun gargadi mutane da su kaurace wa kauyukan da a baya suka ba da umarnin ficewa.
Babban Bankin CBN Ya Kara Kudin Ruwa Zuwa Kaso 27.5 Cikin 100
Amurka tare da Faransa sun taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin, wanda majalisar ministocin tsaron Isra’ila ta amince da shi da yammacin jiya Talata.
Shugaban Amurka Joe Biden ya kira tsagaita wutan “Mataki mai mahimmanci… don kawo karshen tashin hankali” a Gabas ta Tsakiya. Ya ce Iran da ‘yan ta’addanta, Hezbollah a Lebanon da kuma mayakan Hamas a Gaza, “sun yabawa aya zakinta” a cikin sama da shekara guda suna fafatawa da sojojin Isra’ila.
Ya ce yarjejeniyar Isra’ila da Hizbullah “an tsara ta ne domin ta zama ta dindindin ta dakatar da yaki.”
-
News2 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News19 hours ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Tsawaita Dakatarwar Da Ta Yi Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomin Rogo, Bagwai Da Bebeji

