News
An Tsige Shugaban Korea Ta Kudu Daga Mukamin Shi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Majalisar Dokokin kasar Korea ta Kudu ta tsige Shugaba mai ci Yoon Suk-yeol saboda ayyana dokar soji na wucin gadi, wadda ta haddasa da zanga-zanga a kasar
Karo na biyu Kenan cikin kwanaki takwas da ’yan majalisar dokokin kasar suka kada kuri’ar neman tsige Shugaba Yoon Suk-yeol.
‘Yan majalisa 204 daga cikin 300 da majalisa ta kunsa suka kada kuri’a goyon bayan tsige shi a yayin da wasu 85 ba su amince ba, uku kuma suka ki jefa kuri’a, sannan an soke kuri’u takwas.
Shugaban ya rasa kujerarsa ne bayan magoya bayan tsige shi sun yi rinjaye a Majalisar.
Majalisa kolin kasar nada wa’adin kwanaki 180 domin amincewa da matakin ko kuma akasin haka.
Shi ma shugaban kasar wanda ke tsaka da wa’adinsa ya bayyana cewa zai garzaya kotu domin kalubalantar matakin .
