Connect with us

News

Gwaman Kano Ya Mika Sunayen Mutum 6 Da Zai Nada A Matsayin Sabin Kwamishinoni

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mikawa majalisar dokokin jihar Kano sunayen mutane shida da ya ke son nadawa a matsayin sabbin kwamishinoni.

Advertisement

Shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Ismail Falgore, shine ya sanar da hakan a lokacin da ya ke karanta wasikar da Gwamnan ya aiko yayin zaman majalisar na ranar Litinin.

 

Sunayen mutanen da aka ambata ya hada da Shehu Sagagi, Dakta Dahiru Hashim, Ibrahim Wayya, Dakta Isma’il Dan Maraya, Gaddafi Shehu, da Abdulkadir AbdulSalam.

Advertisement

Gwamna Abba ya sanar da yin sauye-sauye tare da garambawul ga kunshin majalisar zartarwa domin daidaita tafiyar al’amuran siyasa a mulkin sa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun gwamna Abba, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa garambawul din da aka yi wa gwamnatin ya fara aiki nan take.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending