Connect with us

News

An Bukaci Shugaban Tinubu Ya Fara Hukunta Ministocinsa Da Suke Kin Halartar Taruka –  Majalissa

Published

on

1734528533992

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bukaci Shugaban Kasa  Bola Tinubu da ya gargadi Ministocinsa marasa rikon amana a cikin majalisarsa wadanda suka ki amsa gayyatar Majalisar Dokokin  ba.

 

Advertisement

Akpabio ya ce irin wadannan ministocin da suka ki amsa gayyatar Majalissa basu  dace da gurbin majalisar ministocin Tinubu ba domin girmama  dimokradiyya.

 

Advertisement

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata lokacin da shugaban kasar ya gabatar da kididdigar kasafin kudin shekarar 2025 na Naira Tiriliyan N47.9.gaban  majalisar dokokin.

 

Advertisement

Wadanda suka yi watsi da gayyatar da Majalisar ta yi musu ba dimokuradiyya ba ne don haka ba su da gurbi a gwamnatin Shugaban Tinubu  a cewar Akpabio a gaban  ‘yan majalisar dattawa da na wakilai.

 

Advertisement

 

Ya kuma jadadda bukatar ministoci da Sanatoci su gaggauta amsa bukatun majalisar dokokin kasar domin bayar da bayanan da suka dace dangane da ayyukansu.

Advertisement

 

Shugaban majalisar dattawan ya ce ‘yan majalisar na da ikon da kundin tsarin mulki ya ba su na daukar mataki idan suka ki bayyana a gaban zauren majalisun biyu

Advertisement

 

Tinubu ya samu rakiyar Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume a wajen gabatar da kasafin kudin; da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; da sauran manyan jami’an gwamnati.

Advertisement

 

 

Advertisement

Channel Tv

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending