News
An Sace Wayoyin Hannu Sama Da Miliyan 25 A Cikin Watanni 12 A Naeriya —Rahoto
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Ofishin Kididdiga na Kasa (NBS) ya bayar da rahoton cewa an sace wayoyin hannu sama da miliyan 25 tsakanin Maris 2023 da Afrilu 2024, a cewar Binciken Crime Experience and Security Perception Survey 2024.
Rahoton NBS, mai taken “Crime Experience and Security Perception Survey 2024”, ya nuna cewa kimanin mutum miliyan 17.9 suke da wayoyinsu da aka sace a cikin wannan lokacin.
Satar waya, wanda ta zama wani sabon laifi a Najeriya Rahoto yana nuna cewa daga cikin kowan ce satar waya 10 na wayoyin da aka sace, 7 daga cikin su sun faru a gida ko a wuraren jama’a, inda kashi 11.7% na wadanda suka kai rahoto ga ‘yan sanda suka nuna jin dadin yadda aka gudanar da binciken.
Kasa da kashi 10% na wadanda aka sace wayoyinsu ne suka kai rahoton ga ‘yan sanda, yayin da fiye da kashi 90% suka kasa kai rahoton saboda dalilai daban-daban.
“Kashi 21.4 cikin 100 na ‘yan Naeriya sun bayyana cewa sun fuskanci matsalr sata, kuma mafi yawan laifin sata da aka fi samun shi shine satar waya.”
