News
Kotu Ta Tasa Ƙeyar Mahdi Shehu Zuwa Gidan Gyaran Hali
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An tsare fitaccen mai sharhi daga Kaduna, Mahadi Shehu, a gidan gyaran hali na Kaduna bayan gurfanar da shi a gaban kotun Majistare (CMC 1) da ke kan titin Ibrahim Taiwo, Kaduna, ranar Talata. Ana tuhumar sa da laifuka guda biyu wanda suka haɗa da, haɗin baki, taimakawa da goyon bayan ayyukan ta’addanci, wanda ya ci karo da sashe na 26 (2)(3) na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022, da kuma tada hankalin jama’a, wanda ya saɓa da sashe na 78 na Dokar Penal Code ta jihar Kaduna ta 2017.
Alƙalin kotun, Abubakar Lamiɗo, ya bayar da umarnin tsare Mahadi Shehu a gidan gyaran hali har zuwa ranar 14 ga Janairu, 2025, domin ci gaba da sauraron ƙarar.
Kasar Saudiyya Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Mutum 6 Masu Fataucin Kwayoyi
An zargi Shehu da wallafa wani saƙon da ya nuna cewa gwamnatin tarayya na shirin kafa sansanin sojojin Faransa a Arewa maso Gabas, bisa zargin da shugaban sojojin Nijar, Abdourahamane Tchiani, ya yi. Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta wannan batu.
Bincike daga manyan kafafen yaɗa labarai, ciki har da The Cable, ya tabbatar da cewa bidiyon da aka yi amfani da shi don wannan zargi na bogi ne. An gano cewa bidiyon ya nuna sojojin Najeriya a filin jirgin sama na Bamako yayin aikin ECOWAS na zaman lafiya a Arewacin Mali, kuma an fara wallafa shi a YouTube tun a watan Janairu na 2013.
Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ce ta kama Mahadi Shehu kwanakin baya bayan gudanar da bincike a kan sa, kuma ta gurfanar da shi gaban kotun Majistare domin fuskantar shari’a.
