Connect with us

News

Wani Saurayi Ya Fille Kan Budurwarsa A Nasarawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Ana jimamin kisan wata budurwa mai suna Salome Adaidu, mai shekara 24, wadda ake zargin saurayinta Timileyin da kashe ta a Jihar Nasarawa.

Advertisement

Ƴan sanda sun damƙe Timileyin ɗauke da kan Salome cikin jaka a ranar Lahadi, 12 ga Janairu, a kusa da wata coci.

Ba Mu Fara Rijistar Jarrabawa Ba – JAMB

Bayan bincike, an gano gawar Salome a gidansa, a cikin buhu, bayan an daddatsa ta.

Advertisement

LEADSHIP ta ruwaito cewa ɗan acaɓa ne ya lura da jini na diga daga jakar Timileyin, wanda ya jawo hankalin mutane suka taru suka damƙe shi, kafin a miƙa shi ga ƴansanda.

Mahaifiyar Salome ta yanke jiki ta faɗi da jin labarin, kasancewar ba ta jima da rasa mijinta ba.

Advertisement

Wannan lamarin ya girgiza jama’a, inda suke Allah-wadai da kisan da aka yi wa Salome.

Ƴansanda na ci gaba da bincike kan alaƙar Timileyin da marigayiyar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending