News
Wata Budurwa Ta Cinna Wa Kanta Wuta A Ofishin ‘Yan Sanda Saboda Saurayin Ta Ya Yi Aure
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata Budurwa ‘yar shekaru 30 da haifuwa ta cinna wa kanta wuta a ranar Alhamis kusa da ofishin ‘yan sandan Sarai saboda takaicin rashin samun damar auren mutumin da take so.
Rahotanni na nuni da cewa jami’an ‘yan sanda biyu Kapil Sandhu dabkuma Abhimanyu suma sun gamu da konuwa a hannayensu a kokarin kashe wutar, in ji Sufetan ‘yan sanda KK Bishnoi.
Makaman Da Ke Hannun Ƴan Ta’adda da ƴan bindiga A Najeriya Mallakin Gwamnatin Tarayya
Jami’in ya ce Budurwar mai suna Nazia ta shigar da kara a ofishin ‘yan sanda na Sambhal inda ta ce tana da alaka ta soyayya da wani Gul Azeem tsawon shekara biyu kuma tana son aurensa.
Haka zalika An gano cewa Gul Azeem yana aiki a Punjab, in ji shi.
Daga baya sai Budurwa ta sake zuwa ofishin ’yan sanda ta ce idan ba suyi masu aure ba da Gul Azeem ta yi kokarin kashe kanta,
An dai bayyana halin da matar ke ciki, kuma tana samun sauki a wani asibiti.
SHO Anuj Kumar Tomar ya ce an yi rajistar FIR akan Gul Azeem a karkashin sashe na 69 na BNS (jima’i ta hanyar yaudara) kuma ana kan bincike a kan lamarin.
