News
Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 1.289 A Cikin Watan Satumba
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kwamitin rabon asusun tarayya (FAAC), a taron sa na watan Oktoban 2024, da ministan kudi, kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun ya ke jagoranta, ya ce ya raba zunzurutun kudi har Naira Tiriliyan 1 da biliyan 298 ga matakai uku na gwamnati a matsayin rabon tarayya na watan Satumba, 2024 daga jimillar Naira Tiriliyan 1.298.
Gwamnatin Tarayya ta karbi Naira Biliyan 424.867, sai kuma Jihohi da suka karbi Naira Biliyan 453, yayin da kananan hukumomi suka rabauta da Biliyan 329 da miliyan 864. Sai kuma jahohin da ake hako man fetur suka rabauta da Naira Biliyan 90 da miliyan 415.
Wata Budurwa Ta Cinna Wa Kanta Wuta A Ofishin ‘Yan Sanda Saboda Saurayin Ta Ya Yi Aure
A jawabinsa na bude taron, Mai Girma Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun, ya jaddada kudirin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiwatar da manufofi, da tsare-tsare da za su habaka samar da kudaden shiga da nufin bunkasa kasa baki daya. jin dadin ’yan Najeriya daidai da zamani.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
