Connect with us

News

Hukumar Hisbah Ta Kama Kwamishina Bisa Zargin Sa Da Lalata Da Matar Aure A Kano

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Rundunar Hisbah ta Kano ta kama wani kwamishinan Jigawa bisa zargin sa da lalata da matar aure.

Advertisement

Kwamishinan da hukumar ba ta bayyana sunansa ba, ya shiga hannu ne bayan ƙarar da mijinta ya shigar, inda yake zargin matar kuma uwar ’ya’yansa biyu na lalata da kwamishinan a bayan idonsa.

Gwamnatin Tarayya, Jihohi, Kananan Hukumomi Sun Raba Naira Tiriliyan 1.289 A Cikin Watan Satumba

Wani jami’in hukumar ta Hisbah da ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana na cewa sun kama kwamishinan da matar ne bayan jami’an Hisbar da mijin matar sun rutsa su a wani kango mallakin kwamishinan a cikin mota.

Advertisement

Ganin su ne kuma ya sanya matar ta yi yunƙurin guduwa a motar, inda ta buge mai gadin, kafin rundunar  Hisbah ta samu nasarar tsayar da ita da nasu motocin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending