Business
Mun karya darajar Naira don mu samu shigowar ɗimbin daloli a hada-hadar Najeriya – Gwamnan CBN
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa darajar Naira ‘ta faɗi warwas”.
Cardoso ya bayyana haka a ranar Laraba, wurin Taron Majalisar Ƙolin Tattalin Arzikin Ƙasa (NESG) 2024.
“Mu na da yaƙinin cewa a yanzu darajar Naira ya ragu sosai, kuma hakan wasu matakai ne da aka ɗauka a ɓangaren hada-hadar kuɗaɗe domin samar da farashin kankankan nan gaba kaɗan.
“Wannan tsari da muka bijiro da shi, zai taimaka wajen samar da farashin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje wanda zai wanzar da daidaito,” inji Cordoso.
Kwanan nan dai darajar Naira ta faɗi warwas inda ake sayar da Dala 1 kan Naira Naira 1,372 a kasuwar ‘yan canji.
Premium Times ta ruwaito cewa a farashin gwamnatin tarayya kuma ana Dala 1 na Naira 878.
Cardoso ya ce yin hakan zai samar da daidaiton farashin canji, kuma zai samar da ƙarin samun daloli ta hanyar haɗa hannu da Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe da kuma NNPCL domin ƙarfafa hada-hadar Dalaa cikin ƙasa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
